✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu safarar doya zuwa Turai sun nemi a cire musu haraji

Masu ruwa-da-tsaki a harkar fitar da doya zuwa Turai sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta kulla yarjejeniya da Kungiyar Tarayyar Turai kan ta cire musu harajin…

Masu ruwa-da-tsaki a harkar fitar da doya zuwa Turai sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta kulla yarjejeniya da Kungiyar Tarayyar Turai kan ta cire musu harajin doya da suke kaiwa kasashen Turai.

Sun mika koken nasu ne cikin takardar bayan taro da suka gudanar a Abuja ranar Lahadin da ta gabata, taron da aka shafe kwana 4 ana yi domin kara wa juna ilimi,ya hadar da takwarorinsu na kasar Ghana.

Takardar wacce Shugaban Kungiyar Manoman Doya, Sarrafata da  Fitar  da Ita Waje, Mista Simon Irtwange ya sa mata hannu, ta ce masu ruwa-da-tsakin suna fuskantar haraji na Yuro 9.5 a kan kowane kilo 100, ya ce ba kamar takwarorinsu na kasar Ghana ba su, saboda yarjejeniyar da kasarsu ta kulla da Turai yanzu kyauta suke kai hajar tasu.

Kamar yadda suka ce babban hikimar taron ita ce su samu musayar bayanai da takwarorinsu na kasar Ghana ta yadda za su inganta harkokinsu wajen fitar da kaya mai inganci.

Kungiyar ta kara da cewa taron, taro ne lalubo hanyoyin bunkasa fitar da doya zuwa kasashen waje, inda harkar doya za ta zama wata hanya ta bunkasa tattalin arzikin Najeriya, kuma ta habaka hada-hadar kudaden ketare.

Sun ce ya kamata Gwamnatin Tarayya ta samar da wani tallafi na musaman ga masu harkar fitar da doya zuwa ketare ta hanyar hukumar kula da fitar da kaya zuwa ketare (NEPC) da kuma Bankin Fito (NEDIM).