Da Dumi Dumi

Matar alkali ta kashe yaron mijinta a gabansa

Matar Alkalin Kotun Majistare da ke Nafada a Karamar Hukunar Nafada a Jihar Gombe, Barista Aliyu Abubakar mai suna Fatima Ardo Chindo Abubakar ta kashe yaron mijinta ta hanyar soka masa wuka, a daidai lokacin da  alkalin ke gida.

Kamar yadda Aminiya ta kalato, marigayin mai suna Hamza Adamu da ake kira da Awilo, ya gamu da ajalinsa ne lokacin da ubangidansa, Alkali Aliyu Abubakar ya kira shi ta waya a ranar Lahadin makon jiya, ya aike shi ya sayo masa ruwan gora na Faro da Maltina da Indomie ya kawo masa gida.

Cikin fushi da matar alkalin ta ga ledar da Hamza ya shigo da ita gidan sai ta tambaye shi mene ne wannan? Sai ya ce mata alkali ne ya ce ya sayo masa. Sai ta ce ashe da shi ake hada kai za a kashe mata aure, sai ta fara zage-zage. Sai ta faki idonsa ta gatsa masa cizo har sau uku a hannu. Da ya ji zafi sai ya ture ta, shi ne ta ciro wata wuka da take jikinta ta daba masa a kirji, ya yi kara ya fadi kasa.

Karar da ya yi ne makwabta suka fito don jin abin da ke faruwa, inda matar da suke gida daya ta tashi mijinta kan ya je ya raba fadan alkali da matarsa. Sai dai zuwan makwabcin ke da wuya sai ya ji matar tana cewa “Na gama da shi, na kashe shi.” inji majiyarmu.

Hakan na faruwar aka sanar da ’yan sanda, inda suka zo suka dauki Hamza zuwa asibiti cikin jini, kuma kafin a je ya cika.

ADVERTISEMENT

Aminiya ta gana da iyayen marigayin, inda mahaifiyarsa mai suna Hajiya A’isha Manzo da ake kira Hajja Manja ta ce ba su yafe ba, suna jiran yadda shari’a za ta yi aiki a kan alkalin da matarsa da ta kashe mata da a gabansa, bai ce komai ba.

Ta ce “Hamza dana ne kuma shekararsa 40 da haihuwa. Shi kadai Allah Ya ba ni a duniya, daga shi ban sake haihuwa ba kuma yaya za a yi a kashe mini shi ba tare da an hukunta mai laifin ba?”

Ta ce Hamza yana gida tare da matarsa A’isha yana cin zogale da misalin karfe goma saura na dare, sai alkalin ya kira shi ya ce masa ya shigo Nafada ya sayo masa Faro da Maltina da kuma Indomie; domin ba zai ci abincin da matarsa ta dafa ba. Ta ce haka ya tsallake zogalen ya je ya aiwatar da aikin ubangidansa, abin da ya zame masa ajali.

“Lamarin ya faru ne da misalin karfe goma da minti bakwai na dare, kuma ba za mu yafe ba, domin tun daga lokacin da matar ta kashe mini da, alkalin bai zo ya yi mana ta’aziyya ba, bai kuma ko kira a waya ba. Haka bai kira matar mamacin ba har yanzun nan,” inji mahaifiyar marigayin.

Ta ce mahaifin marigayi Hamza, Malam Adamu yana zaune ne a Jihar Katsina, kuma da aka gaya masa al’amarin ya ce zai bi kadi, ba zai bari ba.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin mijin Fatima, Majistare Aliyu Abubakar amma lamarin ya faskara.

Amma Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe, DSP Mery Obed Malum, ta tabbatar da faruwar lamarin sai dai ta ce har yanzu suna gudanar da bincike a kai.

Share