✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar Gwamnan Neja ta horar da mata 200 sana’o’i a Suleja

Uwargidan Gwamnan Jihar Neja, Dokta Amina Abubakar Sani Bello ta koyar da mata sana’o’in dogaro da kai a Karamar Hukumar Suleja a karkashin shirinta na…

Uwargidan Gwamnan Jihar Neja, Dokta Amina Abubakar Sani Bello ta koyar da mata sana’o’in dogaro da kai a Karamar Hukumar Suleja a karkashin shirinta na tallafa wa mata da  take gudanarwa a kananan hukumomin jihar.

A ranar Asabar da ta gabata ce aka kammala koyarwar na mako guda, inda aka koya wa matan hada man shafawa da sabulun wanka da wanki da kuma man gyara gashi.

Da take jawabi yayin rufe koyar da matan da suka samu horon, Matar Gwamnan, wacce Matar Kwamishinan Kasuwanci da Zuba Jari Hajiya Mairo Muhammad Mudi ta wakilta, ta ce manufar wannan shirin ita ce a horar da mata sana’o’in da za su dogara da kansu

Ta mika godiyarta ga Uwargidan Gwamnan bisa goyon baya da kulawar da take bai wa mata a jihar. Sannan ta yi kira ga mata su yi amfani da ilimin da suka samu wurin sarrafa shi ta yadda zai amfane su da sauran al’umma baki daya.

A jawabin, wakilin Gwamnan jihar kuma Kwamiahinan Kasuwanci da Zuba Jari, Alhaji Muhammad Mudi ya ce Gwamna Abubakar Sani Bello na bakin kokarinsa wajen ganin ya ci gaba da samar da aikin yi ga mata da matasa domin rage rashin aikin yi a  jihar.

Kwamishinan ya gabatar da takardun shaida ga matan da suka samu horon, da kuma fom da za su cika domin samun tallafi daga gwamnatin jihar da kuma samun bashi daga bankuna idan sun bukaci haka.

Taron da aka gudanar a harabar makarantar firamare ta Auwal Ibrahim da ke Suleja ya samu halartar manyan ’yan siyasa da suka hada da Alhaji Saleh Santana da Shu’aibu Umar da Alhaji Garba D. Biba da Jibrin Yakubu da Ishak Ability da sauransu.