✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar Kobe Bryant za ta kai karar kamfanin helikwaftan da ya kashe mijinta da ’yarta

Matar tsohon dan kwallon kwando na Amurka marigayi Kobe Bryant, Misis Banessa Bryant, wanda ya rasu tare da ’yarsu mai suna Gigi a hadarin jirgin…

Matar tsohon dan kwallon kwando na Amurka marigayi Kobe Bryant, Misis Banessa Bryant, wanda ya rasu tare da ’yarsu mai suna Gigi a hadarin jirgin helikwafta a Kalifoniya na Amurka a ranar 26 ga Janairu ta ce ta shirya tsaf don kai karar kamfanin saboda sakaci wajen gudanar da aiki.

Banessa Bryant wadda mijinta Kobe Bryant ya rasu a wannan mummunan hadarin jirgin helikwafta da ya rutsa da shi da ’yarsu Gigi da wadansu mutum bakwai a Amurka, ta ce ta yanke shawarar kai kwarar kamfanin ne musamman matukin jirgin saboda yin sakaci a ranar da hadarin ya faru. Ta ce rahotanni sun nuna matukin jirgin yana gyangyadi ne  lokacin da al’amarin ya faru wanda hakan ya jefa rayuwar daukacin mutanen da ke cikin jirgin a cikin hadari.

Ta kara da cewa kamfanin da ya mallaki jirgin helikwaftan bai bi ka’idojin tashi a ranar da al’amarin ya faru ba, don a ranar rahotanni sun tabbatar da cewa babu yanayi mai kyau saboda hazo amma duk da haka ya amince jirgin ya tashi wanda hakan ya yi sanadiyyar rasuwar mijinta da ’yarsu da wadansu mutum bakwai.

“Ba zan taba amincewa da wannan sakaci da kamfanin ya yi ba, don haka ne na yanke shawarar shigar da kara don a bi min kadi,” inji Banessa a wani rahoto da kafar watsa labarai ta Naijanews.com ta ruwaito.