Search
Subscribe
Matasa a Shekara daya da rantsar da gwamnatin canji

Matasa a Shekara daya da rantsar da gwamnatin canji

Abubuwa da dama ne suka sa dan Najeriya neman “canji” tun daga: rashe-rashen da suka yi wa ’yan Najeriya yawa, irin su: Rashin wadatacciyar wutar lantarki, rashin ingantaccen tsarin kiwon lafiya, rashin ilimi da rashin ayyukan yi, musamman ga ’yan uwa matasa. Ga kuma cin hanci da rashawa da ina ganin duniya kaf, ba kasar da ta kama kafar yaya babba wato Najeriya. Sai kuma rashin iya mulki da rashin tsaron da ya zama karfen-kafa a kowane lungu da sakon kasarmu.
Wannan ne ya tilasta wa ’yan Najeriya neman canji ruwa-a-jallo. Kuma suka yi amfani da damar da suke da ita wajen kawar da waccan gwamnatin da karfin kuri’unsu.
Bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya sha rantsuwa da Alkur’ani Mai girma, tare da tabbatar da zai yi mulki da adalci bakin ikonsa tare da bin kundin tsarin mulkin kasa sau-da-kafa, da dama daga cikin jama’ar Najeriya, ba su zaci haka lamuran za su gudana, ba, musamman masu tunanin al’amura za su zo cikin sauki, ko su canja a dare daya.
Ko shakka babu duk dan Najeriya mai kishin dorewar kasar a matsayin kasa daya, dole ya jinjina wa Shugaba Muhammadu Buhari, musamman a bangaren yaki da ‘yan kungiyar Boko Haram, ganin yadda gwamnati ta yi galaba a kansu, wanda duk wani dan Arewa maso Gabas zai tabbatar da haka. Sai kuma kyautata huldar kasarmu da kasashen duniya, wanda hakan zai bunkasa tattalin arziki da kimar ’yan Najeriya da a da ta fadi warwas. Sai kuma yunkurinsa na yaki da cin hanci da rashawa ta hanyar samar da asusun bai-daya (TSA), wanda hakan ya taimaka matuka a wajen takaita cin hanci da rashawa das ace kudin gwamnati a kasar nan.
Wannan ke nan, sai kuma wani hanzari ba gudu ba, ko shakka babu akwai jan aiki a gaban shugaba irin na Najeriya, musamman wannan lokacin da tattalin arziki da abubuwa da dama suka dame. Don haka ya zama dole kowane shugaba Buhari ya yi aiki tukuru. Alhamdulillahi Shugaba Muhammadu Buhari yana kokarinsa a kan hakan. Roko ko fatarmu dai Allah Ya ba shi ikon ceto talakawan Najeriya daga cikin halin matsin da muke ciki.
Daga karshe muna rokon Allah Ta’ala Ya iya masa, Ya yi masa jagoranci nagari, Ya cika masa burinsa na alheri, Ya kawar da duk wani mai yunkurin kawo matsala ga wannan gwamnati, Ya kawar da duk mai bakar manufa a cikin wannan gwamnati. Ya Allah muna rokoKa ci gaba mai dorewa.
Abdulmalik Sa’idu Mai Burodi, Tashar Bagu Gusau,  Jami’in Hulda da Jama’a na kungiyar Muryar Talaka, Reshen Jihar Zamfara.
 08069807496.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin