✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar rashin bayyanar da soyayya

Assalamu alaikum makarantanmu, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatar Allah Ya amfanar damu dukkan bayanan da zac su zo cikinsa, amin.…

Assalamu alaikum makarantanmu, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatar Allah Ya amfanar damu dukkan bayanan da zac su zo cikinsa, amin. Ga bayani kan matsalar rashin bayyanar da soyayya a tsakanin ma’aurata da hanyoyin magance su. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.

Wannan matsala ta rashin bayyanar da soyayya ta zama ruwan dare a cikin rayuwar auratattar Hausawa, ta yadda ma’aurata kalilan ne suke rayuwar aure mai cike da nuna so da kauna a cikinsa. Ko a cikin iyali duka, za a tarar yara kanana ne kadai ke samun dadaddiyar soyayya ta hanyar wasan da ake musu, yawan runguma da sumba; kalamai masu dadi da yawan yaba musu da sa su murna ta hanyar murmushi da dariya; idan ransu ya baci kuwa nan da nan za a lallashe su, kuma ko sun yi laifi ba a rikonsu da laifin har ya sa a daina bayyanar masu da kaunar da ake musu. Amma su ma din suna girma irin wadannan abubuwa suna raguwa har sai ta kai soyayyar da ake nuna musu kadai ita ce ta samar musu da duk abubuwan bukatarsu amma ba irin dadadan abubuwan da akan yi musu da suna kanana ba. In muka yi nazari za mu fahimci duk dan Adam na bukatar irin wannan dadadan abubuwa, ba dan Adam kadai ba, duk halittun Allah (SWT) suna bukatar kulawa irin haka.

Wannan fili ya yi ta samun koke-koken wadansu daga cikin ma’aurata kan yadda suke fuskantar wannan matsala daga wajen abokan aurensu.

In muka yi nazari za mu fahimci cewa haka abin yake a mafi yawa na daga cikin ma’aurata Hausawa; yawanci dukkan ma’aurata ba su damu da bayyanar da so da kauna ga junansu ba, ta hanyar kalamai masu dadi da suka dace; wasanni da barkwanci, kulawa ta musamman da sauransu. Ko kuma ya kasance daya daga cikin ma’aurata na kokarin bayyanar da soyayya, amma daya bai nuna jin dadinsa balle har shi ma ya yi kokarin yin irin yadda ake masa.

 

Abubuwan da ke hana bayyanar da soyayya

Al’ada: Yanayin al’ada na taka muhimmiyyar rawa sosai wajen rashin bayyanar da soyyaya a cikin rayuwar aure; a al’adance ba wata soyayyar da ake yi da ta wuce namiji ya samar da kayan bukatun rayuwa ita kuma mace ta kula da gida da yara; kowa yadda ya tashi ya ga ana yi a gidansu, a garinsu, haka zai yi, wanda ko duk aka ga ya fita daban ta hanyar yin abubuwan nuna kauna da kulawa nan da nan za a samu wani lakabin da aka yi masa saboda hakan.

Halin mazantaka: Yanayin halayyar namiji ta sa ya fi iya nuna soyayyarsa da kulawarsa ta bangare daya kawai, shi ne ta hanyar sadaukar da dukiyarsa, lokacinsa da karfinsa ga iyalinsa; wannan kam lallai shi ya fi muhimmanci kuma ya fi amfani, amma dayan da ba su cika yi ba, shi ya fi dadi da sa kwanciyar hankali da aminci a zuciya.

Tsoro: Wannan shine ja gaba daga cikin abubuwan da ke hana ma’aurata bayyanar da soyayya a tsakaninsu; yawanci ma’aurata maza na ganin bayyanar da soyayya, kamar bayyanar da rauninsu ne, kuma hakan zai sa matan su raina su ba su ganin kimarsu. Su kuma matan na tsoron in su cika bayyana soyayyarsu, mazan za su dauke su ba bakin komai ba, kuma ba za su samu irin kulawar da suke so ba daga gare su.

Rikon laifi: Kasawar wadansu ma’aurata ga yafe laifin da abokan aurensu suka yi musu na hana su iya bayyanar da soyayyarsu, domin rikon laifi na dakushe soyayya ko ya sumar da ita gaba daya.

 

Rashin kayan cajin kauna:

Kayan cajin kauna su ne abubuwan da ke dumama so da kauna da zafafa soyayya a tsakanin ma’aurata; sun kunshi yawan runguma da sumbatar juna, musamman lokacin gaisawa, lokacin tarbar juna da lokacin yin ban-kwana. Sai kallo da hararar masu bayyanar da so da kauna; murmushin nuna kauna da sauransu. Yanayin al’adar Bahaushe ta sa kwata-kwata babu abubuwan dumama soyayya da bayyana kulawa wajen wanzar da dangantakar auratayya. Wadansu ma’auratan ko a wajen ibadar aurensu ba su yin wadannan abubuwan caja soyayyar; don haka akwai da yawan ma’auratan da har su gama rayauwarsu ba su taba sumbatar juna ba. Sannan ba su rungumar juna don nuna kauna kawai ba runguma ta sha’awa ba. Ya kamata Malam Bahaushe ya aje al’adarsa ta rashin wadannan kayan cajin kauna cikin auratayya; ya aro daga Larabawa da Turawa sannan ya al’adantar da ita cikin rayuwar aurensa. Ko kuma dabbakar da ita a matsayinta na kyakykyawar Sunnar Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) kamar yadda aka dabbaka sunnar yin musabaha yayin gaisawa da juna; domin wadannan abubuwa suna da matukar alfanu wajen gina aure da inganta shi; sannan ga shi kasancewarsu ibada ce domin suna daga cikin Sunnar Manzon Allah Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi.

Da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a koyaushe, amin.