✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ministoci 20 suka halarci taron majalisar zartarwa a yau

A halin yanzu mataimakin shugaban qasa Yemi Osinbajo ne ke jagorantar taron majalisar zartarwa FEC, a fadar shugaban kasa, a Abuja. Wakilinmu a fadar shugaban…

A halin yanzu mataimakin shugaban qasa Yemi Osinbajo ne ke jagorantar taron majalisar zartarwa FEC, a fadar shugaban kasa, a Abuja.

Wakilinmu a fadar shugaban kasa, ya ruwaito cewa shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya jagoranci taron majalisar na makon jiya, ya tafi zuwa jihar Borno, dan ziyarar aiki. Sa’annan wani lokaci a yau, zai fita zuwa kasar Burtaniya, wanda tafiya ce ta kashin kai.

Wakilin na mu, ya bayyana cewa, an fara gudanar da taron jim kadan bayan isowar mataimakin shugaban kasar zauren taron da misalin karfe 11:01.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, da shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Winfred Oyo-Ita da ma wasu Ministoci 20, ne suka halarci taron.