✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu ma ana kawo mana almajirai masu coronavirus —Ganduje

Gwamnatin Kano ta mayar da martani ga jihohin da ke korafin cewa ta mayar musu da almajirai masu dauke da kwayar cutar coronavirus, tana cewa…

Gwamnatin Kano ta mayar da martani ga jihohin da ke korafin cewa ta mayar musu da almajirai masu dauke da kwayar cutar coronavirus, tana cewa ita ma ana kawo masu cutar.

Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a kan halin da kwamitin kar ta kwana kan annobar ke ciki.

Gwamnan ya bayyana cewa mayar da almajirai jihohinsu na asali batu ne da aka yanke hukunci a kai a taron gwamnonin Arewa.

“Mun yanke hukunci a taronmu na gwamnonin Arewa cewa kowace jiha za ta mayar da almajiran jihar garuruwansu na asali, kuma jihar Kano ta yi aiki da wannan umarni da kyakkyawar niyya,” inji Gwamna Ganduje.

A cewarsa, kamar yadda Kano ke mayar da almajiran da ke yankinta jihohinsu na asali, haka ita ma take karbar nata daga wasu jihohin.

Ya ce ita ma jihar Kano ta samu wasu almajiran da aka dawo mata da su da sun kamu da cutar coronavirus, sai dai ita ta zabi ta yi shiru da bakinta duba da cewa ba surutu almajiran ke bukata ba illa samun kulawa da lafiyarsu.

“Mu ba mu iya surutu ko siyasantar da lamura ba. Mun samu almajiran da aka dawo mana da su suna da wannan cuta bayan mun gwada su sai muka killace su don shi ne kadai abin da suke bukata ba wai a yi ta yayata lamarinsu ba.

“Akwai bukatar mutane su fahimci cewa ba wai yadda ake jigilar almajiran ba ne ya sanya suke kamuwa da cutar,” inji shi.

A cewarsa gwamnati tana bin duk matakan da suka kamata wajen jigilar almajiran.

Rahotanni sun bayyana yadda jihohin Kaduna da Jigawa suke korafi cewa almajiran da aka mayar musu da su jihohinsu daga Kano suna dauke da cutar ta COVID-19.