✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun gamsu da salon shugabancin Aminu Tambuwal – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce sun gamsu da irin salon shugabancin da shugaban Majalisar Wakilai Alhaji Aminu Waziri tambuwal yake gudanarwa…

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce sun gamsu da irin salon shugabancin da shugaban Majalisar Wakilai Alhaji Aminu Waziri tambuwal yake gudanarwa a kasar nan.
Sarkin Musulmi ya bayyana haka ne a ranar Litinin da ta gabata a fadarsa lokacin da yake nada sababbin uwayen kasa 21 daga cikin 23 da gwamnatin Jihar Sakkwato ta kirkiro a jihar, inda ya ce: “‘mun gamsu da aikin Aminu Waziri na alheri da yake gabatarwa.”
Mai alfarman ya ci gaba da cewa: “kokarin da kake yi mun ga ya dace mu karrama ka da wata sarauta don haka a yau muna sanar da kai mun ba ka sarautar Matawallen Sakkwato, kuma biki zai biyo bayan shirin da za mu yi.”
Da Sarkin Musulmin ya juya ga uwayen kasar da aka nada ya shaida musu cewa wannan sarautar da Allah Ya ba su zabin Allah ne don haka su yi wa jama’a hidima kuma su dauki kowa daya.
Ya shawarci wadanda suka yu takara tare da su amma ba su samu nasara ba, su dauki hakan daga Allah ne, Wanda Shi kadai ke iya ba su, don haka su rungumi kaddara su taimaka wa wadanda Allah Ya aza wa nauyin.
Aminiya ta samu labarin cewa mutum biyu da ba a nada ba, daya ya rasu ne, na biyun kuma shugaban majalisar jihar ne wanda ba a bayar da dalilin rashin nada shi ba.