✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun jinjinawa alhazan Kaduna bisa hakuri a Makka – NAHCON

Shugaban Hukumar Aiki Hajji ta Kasa Barista Abdullahi Muktar ya yabawa alhazan jihar Kaduna a bisa yadda suke hakuri tare da biyayya ga shugabaninsu a…

Shugaban Hukumar Aiki Hajji ta Kasa Barista Abdullahi Muktar ya yabawa alhazan jihar Kaduna a bisa yadda suke hakuri tare da biyayya ga shugabaninsu a kasa mai tsarki.

Shugaban Hukumar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido a sansansin ‘yan jihar Kaduna a sansaninsu da ke muna a kasa mai tsarki a daren Talata.

‎Ya ce, duk da kalubale da alhazan suke fuskanta amma sun ci gaba da yin hakuri tare da mayar da hankalinsu wajen gudanar da ibadansu cikin kwanciyar hankali.

Jim kadan, Shugabar Kwamitin Kula da Ciyar da Alhazai ta jihar Kaduna Hajiya Hadiza Yahaya ta ce, a bana sun samu ci gaba wajen ciyar da Alhazan jihar a kasar ta Saudiya.