✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutanen Arewa ba sa cin gajiyar karatu a Jami’ar NOUN – Farfesa Abdallah

Farfesa Uba Abdallah Shi ne Shugaban Jami’ar Karatu Daga Gida ta Najeriya (NOUN) a tautaunawa da wakilan Aminiya, ya bayyana yadda aka bar Arewa a…

Farfesa Uba Abdallah Shi ne Shugaban Jami’ar Karatu Daga Gida ta Najeriya (NOUN) a tautaunawa da wakilan Aminiya, ya bayyana yadda aka bar Arewa a baya wajen karatu a jami’ar, mussaman ganin jami’ar ta kasance tubali ga al’ummar Arewa. Ya kuma yi magana a kan wani tsari da jami’ar ta bullo da shi domin ci gaban al’ummar Arewa:

Dalibai nawa kuke da su a wannan jami’a kawo yanzu?

A yanzu da nake magana da kai 15 ga ga Yulin bana, muna da jimillar dalibai dubu 536 a wannan jami’a. To sai dai kuma ka san muna da dalibai iri biyu ne a wannan jami’a, akwai daliban da muke kira masu rai da marasa rai wato enrolled da kuma actibe.  Abin da ake nufi da enrolled shi ne, su ne suka kunshi duk wani dalibi da ya shigo cikin jami’ar ya biya kudinsa na rajista. Sai kuma daliban masu rai wadannan su ne dalibai da suka ce su ba za su dauki jarabawa ba. To masu ran nan muna da su guda dubu 105.

Muna son ka kara bayani a kan  dalibai masu rai?

Yauwa, to ka san wani abin sha’awa ga lamarin wannan jami’a shi ne babu ruwanka da jarrabawar share fagen shiga jami’o’i.  haka kuma babu ruwanka da  jarrabawar da jami’o’i kan yi kafin su dauki dalibai. A nan bukatarmu sakamakon jarrabawarka ta sakandare idan har ka samu yawan abin da ake bukata ka ci guda biyar kawai amma a ciki a samu darasin Lissafi da Ingilishi. Shi ke nan sun wadatar. To a nan misalin da zan yi maka don ka gane me ake nufi da dalibai mai daukar jarrabawa shi ne, misali na daya sai wani mutum mai sana’ar A Daidaita Sahu yana tara ’yan kudinsa  kuma ya ga sun taru sannan ya yanke shawara ya sayi fom ya cike kuma ya biya kudinsa na rajista ya fara karatu. Ana nan kuma sai abin ya dan juya ya ga yanzu ba ya samun kudi wadanda za su ishe shi ya ciyar da iyalinsa sannan ya yi karatu. Shi ke nan sai ya zo ya sanar da mu cewa  shi fa ya dakatar da karatunsa. Mu kuma nan za mu rubuta mu aje, kudinsa kuma sunan nan a ajiye nan gaba har shekara takwas duk lokacin da ya ga dama zai iya dawowa ya ci gaba da karatunsa, ba tare da ya yi asara ba. Kai in ma bayan shekara takwas sun kare bai samu sukunin dawowa ba, sai mu ce masa kai ga kudinka tafi ka saka su a wani bangaren ka juya abinka.

Na biyu ka dauka mace ce ta zo ba biya kudi ta yi rajista ta fara karatu sai haihuwa ta zo mata, shi ke nan sai ta jingine karatun har sai ranar da ta samu dama. Na uku ka dauka dai mace ce ta fara karatun sai kawai mijinta ya sake ta ta shiga cikin wani hali n rashin natsuwa, ita ma tana da damar da za ta jingine karatun har sai ta samu natsuwa tukuna sannan ta dawo ta ci gaba da karatunta da dai sauran irin wadannan. To ire-iren wadannan daliban namu su ne muke kira da enrolled, wadanda ka ga dai ga su dalibanmu ne amma kuma ba sa yin karatu. Su kuma actibe su ne wadanda daga duk cikin wadannan da na lissafa din sai wadansu suka zo suka ce su za su zauna jarrabawa. Ka dauki misalign dan acaba din nan dai wanda ya jingine karatunsa saboda watakila ba ya da babur, don ni na fi son in yi misali da dan A Daidaita Sahun nan dai saboda ina tsananin sonsu. To sai kuma Allah Ya taimaka sai ya sake samun wani babur din ya ci gaba da harkokinsa kuma ya dawo ya ci gaba da karatunsa ya dauki jarrabawa to wadannan su ne actibe. Kuma mu makarantarmu ba ta da wani tsayayyen lokaci ko zango na daukar dalibai. Kowane lokaci za mu iya daukar dalibai kuma kowane lokaci dalibi zai iya gamawa amma kuma takardar shaidar gamawa ce sai ranar da muka yaye dalibai za a ba ka ita.

To ta yaya ake gudanar da karatu a wannan jami’a?

Wani abin sha’awa duk wani kwas da muke karantarwa a wannan jami’a suna da sahalewar Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC). Kuma takardar shaidar karatunmu daidai take da ta kowace jami’a. Kuma a kowane kwas da kake son ka karanta akwai darussa da dama, misali a ce kamar 12 da za ka karanta, to idan ka je cibiyar karatunmu  wadanda muna da su da dama har ma a cikin kurkuku.  A halin yanzu a cikin cibiyoyinmu na kurkuku muna da dalibai 539 wadanda kuma duk a kyauta suke karatunsu ba ko kwabo  har su gama digirinsu na uku

To dauka za ka yi kwasa-kwasai 12 a zango farko, kuma dama mu a nan za mu cika maka jika dam da tarin littattafan da suka shafi wadannan kwasa-kwasan mu ba ka tunda dama kai ne za ka yi karatun da kanka, sannan mu fada maka mu hadu a ranar jarrabawa. Iyaka dai in kana cikin karatun wani darasi ka ga wani abu da ba ka fahimta ba, to dama ga adireshi Intanet nan na manyan malamanmu wadanda illahirinsu manyan farfesoshi ne, sai kawai ka tambaye su take kuma za su yi maka karin bayani ko ta waya ko kuma su ba ka lokaci su fada maka ka zo cibiyar don su kara maka haske. To ina kai ka, sai ka ga kwasa-kwasan nan 12 sai ka ce kai a gaskiya ni ba zan iya yin su duka ba. To kawai sai ka zabge wadanda ba za ka iya ba sannan ka zabi wadanda ka ga za ka iya ka ci gaba. Idan zangon karatu ya zo na gaba sai ka ci gaba da wadancan ragowar.

Wane sashi ne na kasar nan suka fi cin gajiyar karatu a wannan jami’a?

To da muka yi nazarin dalibanmu masu rai, bisa sikelin shiyya-shiyya da muka raba wannan kasa sai muka ga shiyyar Arewa maso Gabas ita ce ta karshe. Domin su ne suke da dalibai 3,700 sannan sai Shiyyar Arewa maso Yamma kuma suna da dalibai 6,400. To idan ka hada za ka ga akwai dalibai dubu 10 da100, kuma wadannan shiyyoyin suna da akalla jihohi 13. Amma idan ka je shiyyar Kudu maso Yamma wato shiyyar Yarbawa su 37,000 suka dauki jarrabawa. Ka ga sun ninka wadannan shiyyoyi da muke da su. Kuma kada ka manta sun fi kowa yawan jami’o’i a kasar nan kuma sun fi kowa zuwa nan su roke mu mu je mu kafa musu wata sabuwar cibiya.

Amma a Arewa in ban da Kano da Mustafa Dawaki ya dauki nauyin kafa cibiya a Dawaki da kuma Kawu Sumaila da ya dauki nauyin kafa wata cibiyar a Sumaila, sai Suleiman Aminu Garo ya dauki nauyin kafa guda biyu a Fagge da Kwaciri da kuma Sanata Barau Jibrin da ya dauki nauyi fadada Kwamfuta Santarsa don ta zama cibiyarmu ta takwas a shiyyarsa. Sai kuma Katsina inda Gwamna Masari da kudin aljihunsa ya mayar da gonarsa cibiya, to in ban da su a nan Arewa dai ban san wani kuma da ya dauki nauyin wata cibiya ba. Amma ina son ka sani a halin yanzu muna da takardu na neman  mu je mu bude cibiyarmu ga al’ummomi guda 30 wadanda duk daga Kudu maso Yamma suka fito.

Ko wannan na nuna har yanzu ’yan Arewa ba su farga kan alfanun karatu a wannan jami’a ba?

To mun kafa wani kwamiti don gano dalilan da suka hana mutanen wadannan shiyyoyi namu na Arewa shigowa wannan makaranta sai muka gano cewa  har yanzu a wannan jami’a ba a yin wasu kwasa-kwasai da mutanenmu suka fi karantawa irin su Hausa da Nazarin Addinin Musulunci da sauransu. Don haka  yanzu muke ta kokari. Na biyu da farko an kai wannan jami’a a Legas kuma aka kafa ta a can ana ta kwakula a can ba wanda ya sani. Don haka abu na farko da na yi bayan na kama aiki a ranar 1 ga Maris a ranar 28 ga Maris din 2016 mako uku kacal da kama aikina  sai na ce kowa ya kwaso kayansa mu dawo nan Abuja tunda da ma Shugaban Kasa ya riga ya gina mana wannan makaranta a nan.

Ko kana da kira ga manyan Arewa don su agaza wa matasa su yi karatu?

Ni a nawa ganin ’yan siyasarmu na Arewa ba sa ma son matasanmu su yi karatu. Domin idan suka yi karatu to a ina za su samu ’yan bangar siyasa da masu zuwa su yi musu maula a kofar gidajensu. Saboda haka sun fi so matasan su zauna cikin jahilci yayin da su nasu ’ya’yan na can Malesiya da Singafo suna karatu da cin burodin Fiza na  Naira dubu 6. Duk dan siyasar da ya ji haushi to ya yunkuro, idan kai dan majalisar jiha ce to ka dauki nauyi dalibai 20 daga mazabarka in dan Majalisar Tarayya ne ka dauki nauyin dalibai 40 daga mazabarka in kai Sanata ne ka dauki nauyin dalibai 60 daga mazabarka in har da gaske kuke kuna son a kau da jahilci a tsakanin matasan Arewa.