✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 9,000 sun warke daga coronavirus a Najeriya

Adadin mutanen da suka warke daga cutar coronavirus a Najeriya ya kai dubu tara da bakwai a ranar Lahadi 28 ga watan Yuni. Karuwar wadanda…

Adadin mutanen da suka warke daga cutar coronavirus a Najeriya ya kai dubu tara da bakwai a ranar Lahadi 28 ga watan Yuni.

Karuwar wadanda suka warken na zuwa ne a ranar da aka samu raguwar sabbin masu cutar bayan alkaluman sun yi ta tashin gwauron zabi a kwanaki uku da suka gabata a jere.

Alkaluman Hukumar Yadi da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) sun nuna mutum 490 suka kamu da cutar a ranar Lahadin sabanin 594 da 644 da kuma 779 da aka samu a ranakun 25 da 26 da kuma 27.

Hakan na nufin sama da kashi 36 ne suka warke daga mutum 24,567 da suka kamu tun bayan bullar cutar a

Najeriya.

Zuwa yanzu cutar ta kashe mutum 565 sakamakon rasuwar mutum bakwai a ranar Lahadin.

Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da kokarin bude filayen wasu wuraren taron jama’a a kasar, biyo bayan wasu nasarori da ake ganin an samu a yaki da cutar, da kuma matakan kariya da aka tanada.

Kazalika a ranar ce kuma wasu ‘yan kasar 317 suka dawo gida daga Kasar Birtaniya inda suka makale suka kasa dawowa gida sakamakon bullar cutar da ta tilasta rufe tashoshi da kuma hana shige da fice.

Sai dai kuma wasu jihohin kamar jihar Osun, wadda mutum 10 suka kamu a ranar, na barazanar dawowa da dokar hana fita, muddin yaduwar cutar a jihar ta kara kamari.

Barazanar nata na zuwa ne bayan makamanciyarta da jihar Kaduna ta yi tun da farko.