✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum biyar sun mutu, gidaje 300 sun kone a rikicin kabilanci

Akalla mutum biyar sun mutu, yayin da gidaje sama da dari uku suka kone ko aka rusa su sakamakon wani rikicin kabilanci da ya barke…

Akalla mutum biyar sun mutu, yayin da gidaje sama da dari uku suka kone ko aka rusa su sakamakon wani rikicin kabilanci da ya barke tsakanin al’ummar Inyima da ke karamar Hukumar Yakurr  da ta Adun a karamar Hukumar Obubra a Jihar Kuros Riba.
Rikicin, wanda ya faro tun a shekarar 1989, ya sake tashi ne yayin da wani daga cikin mutanen garin Adun ya je gonarsa, bai sani ba ashe wasu mutane sun yi kwanton-bauna, suka mamaye shi suka kama, bayan sun lakada masa duka, suka mika shi ga jami’an tsaro.
Wannan lamari ya harzuka mutanen Inyima, suka daura damarar kwato dan uwansu, karshe har ta kai su ga far wa juna da kisa da duka tare da kone-kone.
Daga bisani wakilinmu da ya bi tawagar jami’an tsaro da suka ziyarci kauyukan biyu, ya zanta da wani dattijo mai suna Iyamba Edung, mai shekara saba’in, wanda bayan ya barke da kuka, sai ya ce, “Ba mu san hawa bare sauka ba, sai kawai muka rika jin harbe-harben bindiga cikin dare bayan mun kwanta barci. Ka ga yadda suka kona mini gida, babu inda zan kwanta”.
Ita kuwa wata mai suna EkaBebi da goyonta, cewa ta yi motar mijinta da shagonta aka kona.
Ya zuwa rubuta wannan labari, gwamnatin jihar ta aike da jami’an tsaro cikin shirin ko-ta-kwana domin kawo karshen rikicin.
Wakilinmu ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, DSP John Umoh, wanda ya ce suna ta kokarin daidaita al’amurran, kuma suna bincike, amma babu mutum daya da aka kama.