Da Dumi Dumi

Na kadu da na ji ba sunana a cikin ministoci –  Adebayo Shittu

Tsohon Ministan Sadarwa Mista Adebayo Shittu ya  ce ya yi matukar kaduwa  da mamaki da ya ga babu sunansa a jerin sunayen ministocin da Buhari ya nada.

Adebayo Shittu ya ce bai taba tunanin cewa Buhari ba zai sake ba da sunansa ba a jerin sunayen ministocin da zai nada ba.

A cewarsa “Ko a mafarki ban taba tunanin Buhari ba zai dawo da ni kujerar minista ba. Sai dai kuma ni dama mutum ne mai tawakkali kuma na yi tawakkali ga Allah kuma na yarda da hukuncin Allah. Dole in gode wa Allah a matsayina na Musulmi, Allah ke badawa kuma Shi ne ke hanawa. Shi Allah ne Ya sa na zama minista ko a wancan lokaci kuma ina matukar godiya ga Allah,” inji Shittu

Ya kara da cewa: “Tun bayan kammala karatuna na fada harkar siyasa, na rike mukamai da dama har zuwa wanda na rike wato na nan kusa wato Ministan Sadarwa. Ina yi wa Allah godiya matuka a kan haka.”

Alhaji Shittu ya ce yanzu zai koma ya ci gaba da harkarsa ta aikin lauya, kuma tuni ya bude ofisoshi a Abuja.

ADVERTISEMENT

Idan ba a manta ba Shugaba Buhari ya nada Malam Isah Pantami a matsayin Ministan Sadarwa inda ya canji Adebayo Shittu a ma’aikatar.

Share