✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nada Stanley Buba Kodinetan Jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa ta tada kura

Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa Mista Damishi Barau Luka ya nuna rashin amincewa da nada Mista Stanley Buba a matsayin kodinetan sabuwar Jam’iyyar APC a jihar…

Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa Mista Damishi Barau Luka ya nuna rashin amincewa da nada Mista Stanley Buba a matsayin kodinetan sabuwar Jam’iyyar APC a jihar inda ya ce Mista Stanley Buba ba dan jam’iyyar ba ne.
Mataimakin Gwamnan ya bayyana haka ne a cikin wata takardar sanarwa da Darakatan Labaransa danjuma Joseph ya raba wa manema labarai a Lafiya. Ya ce “kin amincewa da nadin Stanley Buba a matsayin kodinetan Jam’iyyar APC a jihar nan ya biyo bayan korafi ne da mambobin jam’iyyar a jihar ke yi cewa shi ba dan jam’iyyar ba ne. Kuma shi ba daya ne daga cikin mambobin jam’iyyun adawa da suka kafa APC ba, wato CPC da ANPP da ACN. Shi dan Jam’iyyar Labour ne wanda har yanzu ba ta hade da APC ba. Mista Buba yana yankina ne wato mazabar Akwanga, babu wanda ya sanar da ni cewa za a nada shi a kodinetan jam’iyyar mu ta APC balle a nemi shawarata.”
Sai dai a nasa bangaren Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na kasa mai kula da shiyyar Arewa ta Tsakiya Janar Ahmed Abdullahi Aboki (mai murabus) wanda shi ne ya nada Mista Stanley Buba a mukamin, ya bayyana wa wakilinmu ta waya cewa an bi ka’ida a nadin ’ya’yan jam’iyyar a yayin nada Stanley Buba. Ya ce Mista Stanley Buba cikakken dan Jam’iyyar APC ne, inda ya bukaci ’ya’yan jam’iyyar su yi watsi da masu sukar nadin.
Da Aminiya ta tuntubi Mista Stanley Buba game da batun, ya nuna mamakinsa kan yadda Mataimakin Gwamnan ya manta cikin sauri game da yadda shi Stanley ya zaga kusan dukkan yankunan jihar kwanakin baya yana kamfen ga Jam’iyyar APC tun kafin ma a yi mata rajista a matsayin jam’iyya.