Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Nade-naden mukarraban Sanata Lawan na ci gaba da tayar da kura

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan

Nadin mukaman da sabon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya yi, na ci gaba da tayar da kura a jam’iyyarsa ta APC.

Matasan jam’iyyar sun kekasa kasa sun ce ba su yarda da yawancin mutanen da ya nada a matsayin masu taimaka masa ba, suna masu cewa ya gaje su ne daga Sanata Bukola Saraki.

ADVERTISEMENT

Hakan ya sa Sanata Ahmed Lawan ya janye nadin da ya yi wa Festus Adedayo a matsayin mai magana da yawunsa.

Ba a gama da wannan ba, a ranar Lahadi sai ga mutumin da ya nada ya taimaka masa a fannin kafafen sada zumunta na zamani, Olu Onemola ya ajiye mukamin, yana alakanta hakan da cece-ku-cen da nadin ya haifar.

ADVERTISEMENT

Daya daga cikin jagororin matasan APC da suke korafi a kan wannan batu, Alwan Hassan, ya ce sun gamsu da tattaunawar da suka yi da shugaban majalisar. “Dama batun da muke yi shi ne, wadannan mutane wato Festus Adedayo da Olu Onemola sun yi kaurin suna wajen sukar gwamnatin APC da yin kalaman batanci ga Shugaba Muhammadu Buhari da shi kansa Sanata Ahmed Lawan,’’ inji Alwan Hassan.

Nadin mukamai biyar da shugaban majalisar ya kara yi, ya sake fusata matasan Jam’iyyar APC wadanda suke ganin ba su cancanta ba saboda zargin suna sukar gwamnati.

Ya ce “Shi kansa Sanata Ahmed Lawan bai san da batancin da suke wallafawa a shafin Twitter kan Shugaban Kasa sai a yanzu da aka nuna masa… Majalisa ta ’yan Najeriya ce babu dan APC ko PDP ko wata jam’iyya, amma su wadannan mutane suna zagin Shugaban Kasa ne.”

Festus Adedayo, wanda fitaccen dan jarida ne, ya ce bai nemi mukamin ba tun farko, kuma ba zai taba sauya matsayinsa kan yadda yake kallon al’amuran yau da kullum a Najeriya ba.

Za a dai zuba ido don ganin yadda ci gaba da nade-naden mukaman za su kaya a makon nan, inda wadansu ke ganin wadanda suka yi wa jam’iyya halacci ya kamata a nada a mukaman.

Ya yin da wasu kuma ke batun a duba cancanta ba tare da la’akkari da ‘yan jam’iyya mai mulki ko ‘yan hamayya ba.

Tun da farko dai Sanata Lawan ya fara ne da kokarin kare kansa bayan da wasu kafafen yada labarai suka lakaba masa wani labari da ke cewa ya nemi jam’iyyar APC da Shugaba Buhari da su mika mulki ga yankin Arewa maso Yamma a shekara ta 2023.

Wannan ta sa sai da ya fito ya karyata labarin, inda ya ce wani takwaransa ne, wato sakataren APC na jihar Adamawa, ya yi maganar ba shi ba.

Wani jigo a jam’iyyar APC wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa BBC cewa ganin irin ja-in-jar da aka yi kan takararsa da yadda ta ja hankalin ‘yan kasar, wani zai yi tunanin cewa Ahmed Lawan zai yi taka-tsantsan a duk irin abubuwan da zai yi.

“Amma abin mamaki sai ga shi ya fara wa’adin nasa da haifar da rudani. Muna fatan ba za a sake maimaita irin wannan ba,” a cewarsa.

Kawo yanzu dai ba a nada wanda ko wacce za ta maye gurbin Mista Adedayo ba, sai dai da alama ‘yan APC za su zura ido domin ganin mutumin da za a nada a karo na biyu.