Da Dumi Dumi

Neymar ya yi rawa da ’yan mata 26 saboda murnar shiga sabuwar shekara

Shahararren dan kwallon Brazil Neymar ya yi rawa da ’yan mata 26 don murnar shiga sabuwar shekara.

Dan kwallon ne da kansa ya sanar da haka a ranar Talatar da ta wuce a shafin sadarwasa na Twitter.

Neymar wanda yanzu haka yake wasa a kulob din Paris Saint Germain (PSG) na Faransa, ya koma Brazil ne don yin hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Rahotanni sun ce dan kwallo ne ya shirya bikin murnar shiga sabuwar shekara a wani otel da ke Arewacin birnin Rio de Janeiro na Brazil, inda ya gayyaci ’yan uwa da abokan arziki da ’yan mata don su gwangwaje.

Neymar dan shekara 26 kawo yanzu shi ne dan kwallo mafi tsada a duniya bayan da ya canja sheka daga kulob din FC Barcelona zuwa PSG kimanin shekara 2 da suka wuce.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya