✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Obasanjo ya rude, cewar fadar shugaban Najeriya

Fadar shugaban kasar Najeriya ta bayyana cewa, kalaman tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo alama ce ta rudewa. A wani rahoto da mai taimaka wa Obasanjo…

Fadar shugaban kasar Najeriya ta bayyana cewa, kalaman tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo alama ce ta rudewa.

A wani rahoto da mai taimaka wa Obasanjo a harkar watsa labarai Kehinde Akinyemi ya fitar da ke cewa, wanda bai san ciwon kansa  bane kawai zai ci gaba da goyon bayan wannan mulkin da ake yi a Najeriya.

Obasanjo ya ce, wadanda ba su dace ba ne ke jagorancin Najeriya don haka kasar ta lalace, sanadiyyar rashin samun shugabanni nagari wanda suke aiki karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari.