Da Dumi Dumi

PDP ba ta da ikon kai karar ’yan majalisar da suka koma APC – Abdullahi Adamu

Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu ya ce Jam’iyyar PDP ba ta da wani ’yanci a shari’ance na shigar da karar mambobin Majalisar Wakilai 37 da suka sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC, domin ita ta fara cin gajiyar haka.
Sanata Abudullahi Adamu ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Keffi a karshen mako jiya, inda ya ce kuma jam’iyyar ba ta da ikon bayyana kwace kujerar wani dan majalisa.  “A karkashin kundin tsarin mulkin kasar nan, ba za ka ce ni Sanata Abdullahi Adamu ba dan majalisa ba ne. Saboda haka PDP ba za ta iya bayyana rasa kujerar wani dan majalisa ba,” inji shi.
Ya kara da cewa da shi da wasu ’yan Jam’iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa APC sun yi haka ne saboda a cewarsa Jam’iyyar PDP ta kasa cimma manufofinta. Ya ce  “Idan kana bibiyar abubuwan da ke faruwa a kasar nan a bangaren siyasa za ka gano cewa babu wani abin kirki da Jam’iyyar PDP take yi wa al’umma. Al’ummata ta Jihar Nasarawa ya zame mana dole mu kasance cikin taragon ciyar da jiharmu da kuma kasarmu Najeriya gaba.”
Kodayake SanataAdamu na daya daga cikin jiga-jigan Jam’iyyar PDP, matakin da ya dauka a baya-bayan nan na canja sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC, ya ce ya yi haka ne saboda salo da kuma kyakkyawan manufofin da Jam’iyyar APC ke da shi.
“Na ga ya kamata ne in kasance cikin abin da ke da kyau ga jiharmu Nasarawa. Idan Jam’iyyar APC tana da kyakkyawar manufa a gare ni da sauran al’ummar jihar nan da ma kasa baki daya to lallai ya zame dole in koma jam’iyyar,” inji shi.
Sai ya yi kira ga al’ummar jihar da kasa baki daya su fito kwansu da kwarkwata don su kada kuri’unsu ga Jam’iyyar APC a zabubbuka masu zuwa don a cewarsa jam’iyyar ce kadai ke iya samar musu da shugabanci nagari a kasar nan. 

Share