✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP na yunkurin tsige Al-Makura – Bincike

•Ba gaskiya ba ne – Majalisa Jam’iyyar PDP da wasu mukarraban fadar Shugaban kasa na shirya wani yunkuri na tsige Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko…

•Ba gaskiya ba ne – Majalisa

Jam’iyyar PDP da wasu mukarraban fadar Shugaban kasa na shirya wani yunkuri na tsige Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura daga mukaminsa tare da maye gurbinsa da Mataimamkinsa, kamar yadda Aminiya ta samu labara a Abuja a karshen makon jiya.
Tuni Jam’iyyar PDP ta fara zawarcin Mataimakin Gwamnan Damishi Barau Luka ya fice daga Jam’iyyar APC kafin tsigewar, inda daga nan zai karbi ragamar mulki a matsayin Gwamnan PDP domin yi mata aiki ta samu nasara a zaben badi.
Dangantaka ta fara tsami a tsakanin Al-Makura da Mataimakinsa tun karshen shekarar da ta gabata.
An rika gani Luka yana rakubar shugabannin PDP ciki har da Shugaba Goodluck Jonathan wanda suka yi bauta a coci tare a kusa da Keffi a Janairun da ya gabata. Bayan bauta a cocin ne Luka ya soki APC kan kiran wakilanta a Majalisar kasa rika su ki amincewa da kasafi saboda “gadarar” da ake nunawa a Jihar Ribas.
Daga baya Jam’iyyar APC ta jihar ta dakatar da Mataimakin Gwamnan daga jam’iyyar, inda ta kafa hujja
da bayanin da ya yi kan umarnin na APC.
“(Luka) zai koma PDP a lokaci da ake yunkurin tsigewar inda zai zama Gwamna a karkashin PDP. Wannan shi ne abin da aka tsara,” wata majiya da take sane da wannan shiri ta shaida wa Aminiya a Abuja.
Majiyoyi a PDP sun ce an shirya Shugaba Jonathan da sauran jiga-jigan PDP za su halarci wani babban gangami cikin ’yan makonni masu zuwa a Lafiya domin karbar masu ficewa daga APC, cikinsu har da Mataimakin Gwamnan da kuma Sanata Solomon Ewuga.
Ewuga babban aminin Gwamnan Jihar Nasarawa ne kafin rikicin Ombatse a watan Mayun bara, kuma tuni ya bayyana komawarsa Jam’iyyar PDP.
Wani jigo a PDP a Jihar Nasarawa shi ne Ministan Watsa Labarai Labaran Maku, sai dai ba a tabbatar ba kan ko yana da sha’awa a shirin tsige Al-Makura tare dam aye gurbinsa da Luka a matsayin Gwamna karkashin PDP, saboda shi ma Maku yana da sha’awar zama Gwamnan.
Idan Luka ya karbi ragama akwai yiwuwar ya dakile burin Maku na samun tikitin takarar Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar PDP a zaben badi.
Aminiya ta samu bayanin cewa an tsoma ’yan Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa a shirin tsigewar, kuma tuni sun tsara laifuffukan da za su jawo tsige Gwamnan. Jam’iyyar PDP tana da ’yan majalisa 19, yayin da APC ta Al-Makura take da biyar kacal.
Gwamna Al-Makura yana samun matsala wajen aiki da majalisar tun hawansa gadon mulki a watan Mayun 2011. Sai dai ya kokarta haye siradi da dama, amma wani dan siyasa da ke da masaniya kan yunkurin tsigewar ya ce zai yi wuya Gwamnan ya tsallake wannan “gagarumin shiri.”   
Lokacin da aka tuntubi fadar Shugaban kasa a ranar Lahadi da daddare ta ce ba ta shirin ingiza a tsige Al-Makura, amma Luka a kashin kansa ya yanke shawarar komawa PDP.
“Fadar Shugaban kasa ba ta yi zawarci ko ta nemi Mataimakin Gwamnan Nasarawa ya koma PDP ba. Shi Mataimakin Gwamnan ne a kashin kansa ya yanke shawarar komawa PDP, kuma Shugaban kasa ba zai ce a’a ba,” Mashawarcin Shugaba Jonathan kan Harkokin Siyasa Ahmed Gulak ya fadi haka ta tarho.
Ya ce, “Tambayar da ka yi kan fadar Shugaban kasa da PDP suna shirya yunkurin ingiza a tsige Al-Makura, abin d azan iya ce maka shi ne babu wani mai kama da tsigewa.”
Kakakin PDP a Jihar Nasarawa, Mista John Mark Neto, ya ce babu wani bayani a hukumance da ke nuna Luka zai koma PDP, duk da ya tabbatar da jin jita-jita game da komawar Luka jam’iyyar.
Aminiya ta kasa samun Mataimakin Gwamnan ta tarho domin jin ta bakinsa, sai dai kakakinsa danjuma Joseph ya ce bai da masaniya kan yunkurin tsige Gwamna Al-Makura. “Ban san komai kan wannan ba,” ya shaida wa Aminiya ta waya.
Shi ma Kakakin PDP na kasa Olisa Metuh an kasa samnusa domin jin ta bakinsa.
Shi kuma Kakakin Gwamna Al-Makura Malam Iliyasu Ali Yakubu bai tabbatar ko ya musanta akwai shirin tsige Gwamnan ba lokacin da wakilinmu ya tuntube shi. Ya ce Gwamnan ya sha tsallake siradin ’yan majalisar a baya tare da tsayawa kan kafafunsa.
“Taimakon Allah da kuma sadaukarwa da bi ka’idoji da tsarin mulki ne suke kwatar Gwamnan,” inji Yakubu.
“Dalilan da suka kawo Gwamnan gadon mulki su ne irin dalilan suka sa yake mulkin jihar a wadannan shekara uku. Shekara uku ne na kalubale, amma Gwamna ya ci gaba da tsayuwa kan kafafunsa dmoin cimma bukatun raya ci gaban jama’arsa, mutanen Allah,” inji shi.

‘Almubazzaranci da dukiya’
Aminiya ta ruwaito cewa majalisar jihar ta amince da bukatar fara binciken ayyukan Gwamnan tun daga karshen shekarar da ta gabata.
 Kuma a ranar 3 ga Nuwamba, ’yan majalisar sun kafa kwamitin wuci-gadi da zai duba rahotannin da wasu kwamitocin majalisar hudu da suka binciki gwamnatin daga 29 ga Mayun 2011 zuwa Nuwamban 2013 suka gabatar mata.  An umarci kwamitin ya duba rahoton kwamitocin majalisar kan kudaden gwamnati da na kiwon lafiya da na kananan hukumomi da harkokin masarautu da na masana’adantu da kasuwar zuba jari tare da mika wa majalisar rahoto domin dada tattaunawa.
Yanzu haka majalisar ta karbi rahotannin hudu na kwamitocin biyar, kuma kwamitin kudadn gwamnati ya yi zargin kashe kudin da babu a cikin kasafin da suka kai Naira biliyan uku da Gidan Gwamnati da Ofishin Mataimakin Gwamna da Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar suka yi. Sai kuma zargin an kashe Naira miliyan 100 daga cikin Naira miliyan 400 na tallafi ga wadanda ambaliya ta shafa ba bisa ka’ida ba, yayin da aka ajiye Naira miliyan 300 a asusun Hukumar Bada Tallafi ta Jihar.
Kwamitocin uku sun zargi gwamnati da aikata ba daidai bad a kudade ciki har da kashe kudaden da ba su cikin kasafi.
Wani babban jami’in gwamnati ya shaida wa Aminiya cewa batutuwan da kwamitocin suka gabatar ne aka tsara a cikin sanarwar tsigewar tare da karin zargin cewa Gwamnan bai sauke nauyin da ke kansa game da Jami’ar Jihar Nasarawa yadda ya kamata da kuma zargin an sace kudin shirin tallafin rage radadin karin kudin mai (SURE-P). Kuma ’yan majalisa 22 daga cikin 24 ne suka sanya hannu a sanarwar tsigewar inji majiyar.
Sai dai Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta musanta cewa tana yunkurin tsige Gwamna Al-Makura, inda Shugaban Masu Rinjaye Gdoiya Akwashiki da Shugaban Kwamitin Labarai na Majalisar Mohammedn Baba Ibaku suka musanta rahoton da ya ruwaito wasu majiyoyi suna nuna ’yan majalisar na yunkurin tsige Gwamnan.
Akwashiki ya ce ba gaskiya ba ne, inda ya ce sanarwar tsigewar da aka magana an rubuta ta bara ne don haka ba ta nuna halin da ake ciki a yanzu. “Ba za ka sanya hannu kan sanarwar tsigewa ka ajiye ta a kabet ba, hakan bai faru ba,” inji shi.
Shi kuma Baba Ibaku ya ce, “Babu wani shiri na tsigewa; ba mu aiki a kan zato.” Kuma ya ce majalisar ba ta zauna da Mataimakin Gwamna Damishi Luka ba, wanda ake ganin ana shirin ba shi damar cin gajiyar shirin tsigewar idan ta samu nasara.
Game da sakamakon binciken Gwamnan kan zargin kashe kudin da babu su a cikin kasafi da kuma almubazzaranci an sanar da Gwamnan, inda ya kara da cewa, “mun mika kalubalen gare shi ya nuna kurenmu,” inji shi.
Majalisar Gwamnoni ta Najeriya a karkashin Gwamna Rotimi Amaechi na Jihar Ribas ta yi Allah wadai da yunkurin tsige Gwamnan, inda ta ce: “Mun samu labarin Fadar Shugaban kasa tana kulle-kullen ta haramtacciyar hanya ta tsige Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura. Muna Allah wadai da wannan sabon yunkuri na keta tsarin mulkin dimokuradiyya.”