Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Ra’ayi: Ya kamata a ba manoma taki da wuri

Ra’ayi: Ya kamata a ba manoma taki da wuri

Noma tushen arziki. Masu  azancin magana na cewa, ‘na duke tsohon ciniki, kowaz zo duniya kai ya tarar.’ Haka rayuwa ba ta tafiya daidai sai da abinci. Koda yaki ake yi, tilas sai an ci abinci. Saboda haka noma abu ne mai matukar muhimmanci gami da albarka da samun lada mai yawa.