✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Ashura: An yi dauki ba-dadi tsakanin ’yan sanda da ’yan Shi’a

Ranar Talatar da gabata ce ranar 10 ga Muharram kuma Ranar Ashura, inda yayin da mabiya Sunnah suke azumtarta  ’yan Shi’a mabiya Zakzaky a karkashin…

Ranar Talatar da gabata ce ranar 10 ga Muharram kuma Ranar Ashura, inda yayin da mabiya Sunnah suke azumtarta  ’yan Shi’a mabiya Zakzaky a karkashin Kungiyar Harkar Musulunci (IMN) sukan yin jerin gwano ne a sassan  kasar nan da wasu kasashen duniya.

A bana duk da cewa kotu ta haramta Kungiyar IMN ta mabiya Zakzaky kuma rundunar ’yan sanda ta haramta ayyukan kungiyar, ciki har da jerin gwano a fadin kasar nan, almajiran Zakzaky mabiya Shi’a sun yi kunnen shegu, inda suka fito don yin zanga-zangar, wanda hakan ya jawo aka yi dauki ba dadi a wasu jihohin kasar. A Abuja, an yi jerin gwano na minti 30 ne kawai, inda ’ya’yan kungiyar IMN din suka yi gaggawar tashi domin guje wa arrangama da ’yan sanda.

A Jihar Katsina kuwa, jagoran kungiyar, Sheikh Yakubu Yahaya ya ce an kashe musu mutum daya a Malumfashi, sannan mutum 20 suka samu rauni bayan da ’yan sanda suka kai musu hari.

Amma Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, SP Gambo Isah ya ce ba zai yiwu su zuba ido suna ganin ana zanga-zanga cikin tashin hankali ba, “Hakan ya sa jami’anmu suka kama mutum 36 cikin ’ya’yan Kungiyar IMN da aka haramta. Sannan dan sanda daya ya samu rauni a arangama da ’yan Shi’ar a Malumfashi. Kuma za mu gabatar da su a gaban kotu,” inji shi. Haka an samu rahoton arangama tsakanin ’ya’yan Kungiyar IMN ta mabiya Shi’a da ’yan sanda a garin Funtuwa da cikin garin Katsina.

A Jihar Kaduna kuma, Kungiyar IMN ta yi zargin cewa an kashe mata mutum uku, kuma aka jikkata wadansu a Bakin Ruwa da ke kan Titin Nnamdi Azikwe a cikin garin Kadua. Daya daga cikin jagororin kungiyar mai suna Aliyu Umar ne ya sanar da haka, inda ya ce ’yan sandan ne suka kai musu hari a lokacin da suke jerin gwanon jimamin Ranar Ashura.

Amma Kakakin Rundunar ’Yan sandan JiharKduna, DSP Yakubu Sabo ya ce labarin kanzon kurege ne kawai. “Mun samu labarin sirri a kan kungiyar ce, wanda hakan ya sa muka yi gaggawar zuwa inda suke taron, sannan muka kore su.”

Haka kuma wakilanmu sun ruwaito cewa an yi jerin gwanon cikin lumana a Damaturu da Potiskum da ke Jihar Yobe.

Sannan wani jagoran Kungiyar IMN a Jihar Nasarawa, Muhammad Ibrahim Gamawa ya ce sun yi tattakin cikin lumana a garin Lafiya.

A Jihar Bauchi kuwa, mutum shida aka ruwaito an kashe sannan aka jikkata 42.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, DSP Kamal Datti Abubakar ya ce ’yan sanda sun yi kokarin yin aikinsu na tabbatar da doka da oda inda suka hana masu yin zanga-zangar saboda doka ta hana gangami sai da izini. Kuma ya musanta batun kisan kai inda ya ce ba su kashe kowa ba.

Da yake jawabi, Kakakin Kungiyar IMAN a Bauchi, Malam Musa Bayi Mohammed ya ce ’yan sanda a mota 20 sun kai musu farmaki a kusa da Kasuwar Santaral inda suka harbe mutum hudu suka raunata12 bayan haka suka kama mutum 27 suka tafi da su bayan sun musu dukan kawo wuka. Ya ce a garin Azare kuma sun kashe mutum biyu suka raunata 30.

Malam Muhammad  ya ce kungiyar kamar sauran ’yan Najeriya suna da ’yancin gudanar da addininsu ba tare da tsangwama ba kamar yadda dokar kasa ta bukaci kowa ya yi addininsa ba tare da tsangwama ba, amma ’yan sanda suka far  musu duk da cewa ba su shiga hidimar kowa ba kuma ba dauke suke da wani makami.

Mazauna unguwannin Malam Goje, Makera da Tashar Babiye a Bauchi sun koka kan yadda ’yan sanda suka rika jefa barkonon tsohuwa lokacin da suke kokarin tarwatsa zanga-zangar. ’Yan sandan daga baya sun nemi jagororin kungiyar don zama da su kuma su karbi mutanensu da aka kama saboda Gwamnan Jihar Sanata Bala Mohammed ya nuna rashin jin dadin faruwar lamarin.

Kuma w-akilinnamu ya ga wadansu daga cikin shugabannin kungiyar a hedkwatar ’yan sandan da ke Bauchi.