✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar da mawaki Tuface ya kusa halaka a jirgi

A Lahadin da ta gabata ne wani hatsarin jirgin sama ya kusa ritsawa da mawakin nan da ya dade yana fantamawa a duniyar mawakan kasar…

A Lahadin da ta gabata ne wani hatsarin jirgin sama ya kusa ritsawa da mawakin nan da ya dade yana fantamawa a duniyar mawakan kasar nan.
Mawakin, Tuface Idibia, ya shigo jirgi ne daga kasar Afrika Ta Kudu zai zo Legas. Yana cikin jirgi da tawagarsa, yana ta sauraren waka daga na’urarsa sai ya fara jin kaurin waya na konewa. Lamarin ya kara ta’azzara, inda wutar jirgin gaba daya ta dauke. Nan take kuma fasinjoji suka fara karaji, wasu na cewa: “Jirgin nan zai tarwatse!”
Inda abin ya zo da sauki shi ne, lokacin da matukin jirgin ya bayyana cewa lallai jirgin ya samu matsala a bangaren lantarki, don haka fasinjoji su natsu, jirgin zai yi saukar gaggawa. Daga nan ne ya juya akalar jirgin suka koma kasar Afrika Ta Kudu.
Daga nan ne shi kuma Tuface ya yi ta lallashin tawagarsa, yana shawartarsu da cewa kada su razana. Suna isa filin jirgin sai suka yi sa’a kafafun jirgin suka bude, wanda haka ya ba su damar saukowa lafiya. Nan da nan kuwa aka dauke fasijojin, aka canja musu wani jirgin.