Da Dumi Dumi

Ranar Lafiyar Kwakwalwa: ’Yan Najeriya miliyan 60 na fama da tabin hankali

Wani mai tavin hankali da kuma cibiya da dakin kwanansu a Gombe
Wani mai tavin hankali da kuma cibiya da dakin kwanansu a Gombe

Ranar 10 ga watan Oktoban kowace shekara rana ce da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a karkashin Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin Ranar Lafiyar Kwakwalwa domin tunawa da masu tabin hankali a duniya.

A ranar a duk shekara wadda ta kama jiya Alhamis, akan shirya tarurrukan kara wa juna sani da gangami da sauransu domin wayar da kan mutane kan abubuwan da suka shafi tabin hankali, kamar abubuwan da ke janyo tabin hankalin irin su shaye-shayen miyagun kwayoyi da damuwa da sauransu.

Taken ranar na bana shi ne: ‘Kiyaye Kisan Kai.

An kebe wannan rana ta masu tabin hankali ta duniya ce domin wayar da kan mutane game da abubuwan da suka shafi masu tabin hankali kuma an  faro ta ce a 1992, inda Kungiyar Kula da Lafiyar Kwakwalwa ta Duniya (World Federation for Mental Health) ta jagoranci haka bisa jagorancin Mataimakin Sakatare Janar na Kungiyar, Richard Hunter.

Bincike ya nuna cewa Najeriya na da kusan cibiyoyi da asibitocin lura da masu tabin hankali 200 ne kawai, wadanda suka yi karanci matuka wajen lura da mutanen kasar nan miliyan 200, wadanda ciki akwai masu cutar da ke da alaka da tabin hankali da aka kiyasta za su kai miliyan 50 zuwa miliyan 60.

ADVERTISEMENT

Bisa wannan kiyasin, ya zama likitan kwakwalwa daya ne zai lura da mutum miliyan daya, ga kuma rashin asibitoci ko cibiyoyin lura da marasa lafiyar kwakwala. Jihohin da kuma suke da cibiyoyin, yawancin sun lalace kuma ba a lura da su yadda ya kamata. Sai kuma wasu jihohin da suke da asibitocin tarayya da ke kula da masu tabin hankalin.

Wani likitan kwakwalwa da ke Asibitin Kwakwalwa na Royal College da ke Landan ya ce yadda gwamnati take rikon sakainar kashi ga bangaren ne ya sa likitocin bangaren da dama suke ficewa daga kasar nan zuwa inda za a girmama aikinsu.

Rahotanni daga jihohi

A jihohin Kwara da Yobe da Kogi da Bayelsa, Aminiya ta gano cewa babu cibiyoyin kula da masu tabin hankali. A jihohin da akwai kuma, ba a kula da su yadda ya kamata.

A Jihar Kano akwai asibitoci biyu da ake kula da masu lalurar tabin hanalkali da suka hada da  na Goron Dutse da na Dawanau wadanda suke karkashin gwamnatin jihar. Haka kuma akwai cibiyoyin da ake ajiye masu lalurar a wani mataki na gyaran hali wanda suke karkashin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SARERA)

Malam Nura Hussaini ma’aikacin jinya ne a Asibiin Masu Tabin Hankali da ke Dawanau a Jihar Kano ya shaida wa Aminiya cewa suna lura da masu wannan lalura ne ta hanya biyu. “Muna kula da marasa lafiyar ta hanyoyi biyu akwai wadanda ke zuwa su sha magani su tafi akwai kuma wadanda ake ba su gado a asibitin, ya danganta da yanayin ciwon da ya samu mutum. Haka akwai yanayin ciwo da kwayoyin magani kadai ake ba marar lafya akwai  yanayin da marar lafiya ke shiga kamar misali a samu yana duka ko yunkurin hallaka kansa ko mutane, to irin wannan dole sai an hada da allura wacce za ta taimaka wajen sauko da marar lafiyar ya daidiata,” inji shi.

Ya ce a asibitinsu suna kula da masu kwanciya ta hanyar jan su a jiki inda cikin wasa da dariya suke karbar magani su sha ba tare da fuskantar wata matsala daga gare su ba. “Duk tuburewar mara lafiya idan ya zo wurinmu za ki ga ya samu sauki saboda yadda muke mu’amala da su . Mukan ja su jikinmu muna hira da su ba mu kyararsu. Mutane suna mamakin yadda muke zaune lafiya da su, ba wani abu ba ne illa muna girmama su,” inji shi.

Malam Aminu Garba Sulaiman shi ne Shugaban Cibiyar Gyaran Hali da ke kula da masu lalurar tabin hankali da ke Dorayi a Kano, ya shaida wa Aminiya cewa a yanzu haka suna da masu lalurar tabin hankali 130 da ke zaune a gidan kuma gwamnatin Jihar Kano ke daukar nauyin abincinsu da maganinsu da sauaran al’amuran yau da kullum. Ya ce, “A nan ake ba su abinci da wurin kwana. Muna kuma da likitoci da malaman jinya da ke kula da su wajen ba su magunguna. Muna da masu ba su shawarwari don ganin sun dawo kan hanya har a samu su warke, kuma alhamdulillahi kwalliya tana biyan kudin sabulu. Muna samun wadanda suke samun sauki.”

Ya ce yawancin masu fama da lalurar da ke gidan sun hadu da ita ce dalilin shaye-shayen miyagan kwayoyi, “Duk da cewa akwai masu nau’in hauka na gado da wadanda ke samu dalilin shiga damuwa, amma mu a nan gidan wadanda suka samu ta dalilin shaye-shaye ne suka fi yawa wadanda kuma yawancinsu matasa ne,” inji shi.

Da wakiliyar Aminiya ta ziyarci Cibiyar Kula da Masu Tabin Hankali ta Jihar Adamawa, an shaida mata cewa shugaban cibiyar ya yi tafiya kuma shi ne ya kamata ya mata bayani.

A Jihar Kebbi, akwai cibiyoyi  biyu, daya a Jega daya kuma a Zauro. Ta Jega tana karkashin kular Ma’aikatar Mata da Tallafi, ita kuma ta Zauro likitoci sukan zo ne daga Asibitin Kwakwalwa na Tarayya da ke Sakkwato.

A Jihar Nasarawa babu wajen lura da masu lalurar tabin hankali, amma Dokta Ibrahim Ahmad, Darakta a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar ya bayyana cewa sun fi mayar da hankali ne wajen shirye-shiryen wayar da kan mutane kan kiyaye abubuwan da suke jawo lalurar, sannan ya ce za su bude cibiyar nan ba da dadewa ba.

Bayanan masu lura da masu tabin hankali

Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano cewa akwai karancin mahaukata da ke yawo a tituna da kasuwannain Jihar Kano wanda hakan ke nuni da cewa an samu karancin mahaukatan a jihar ko kuma ’yan uwan mahaukatan sun killace su a kusa da su.

Aminiya ta zagaya Kasuwar Kurmi wanda a da a nan ne yawancin mahaukata ke yin dandanzo suna kwana a cikin kasuwar inda ta gano karancin masu wannan lalura a cikin kasuwar.

A Babban Birnin Tarayya Abuja, wakilinmu ya ruwaito karancin mahaukata a kan titunan birnin, inda ya ce yawanci ba a barinsu suna yawo a Abuja, domin ko nakasassu ma ba a cika barinsu ba.

Malam Danliti Muhammad maigadi a Kasuwar  Kurmi  ya yi wa Aminiya karin haske game da yadda masu tabin hankali suka yi karanci a kasuwar. “Kin ga mu ne muke kula da kasuwar nan a yanzu zai yi wahala ki ga wani mahaukaci ya zo kasuwa ya kwana, ko da rana sai ki yini ba ki ga mahaukaci ya shigo kasuwa ba,” inji shi.

Hajiya Rabi Sani wata mata ce da ke kula da mahaifiyarta mai lalurar tabin hankali ta bayyana cewa masu wannan lalura suna son ja a jiki da rarrashi wanda hakan ke sanya su samun saukin ciwon. “Abin da na kula da shi, shi ne masu wannan ciwo suna son rarrashi idan za ka yi musu abin da kake bukata misali wanka da gyaran dakin da suke ciki da ba su magani, to akwai bukatar ka yi musu cikin lallashi ba tare da yi musu tsawa ko kyara ba. Idan suna samun isasshiyar kulawa za ka ga suna samun sauki. Kin ga ni ina sanya mahafiyata ta yi wanka. Bayan ta tafi wanka sai in kwashe kayan da ta cire sannan in gyara mata dakin in share shi. Idan ta dawo sannan in ba ta wankakkun kayanta ta sanya. Ina kuma ba ta abinci mai kyau ta ci sannan ina ba ta magungunanta ta sha. Yawanci idan suna samun kula da abinci isasshe da magani ba za su rika fita yawo kan tituna ko kasuwanni ba.”

Share