✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasha ta kashe fararen hula da dama a Siriya

Fararen hula 11 ne suka rasa rayukansu, sakamakon hari ta sama da jiragen saman Rasha da na gwamnatin Siriya suka kai a yankin Idlib da…

Fararen hula 11 ne suka rasa rayukansu, sakamakon hari ta sama da jiragen saman Rasha da na gwamnatin Siriya suka kai a yankin Idlib da aka hana rikici a cikinsa.

Ofishin sa ido na bangaren ‘yan adawar Siriya, ya bayyana cewar jiragen saman Rasha sun kashe fararen hula tara inda na gwamnatin kasar suka kashe mutum biyu.

Tun shekarar 2011 ake yaki a lardin Idlib na yammacin Siriya inda ‘yan adawa masu dauke da makamai suke arangama da sojojin gwamnati.