✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin Hajiya Habibatu Magaji na Najeriya ne gaba daya Inji Atiku Abubakar

A farkon wannan makon ne aka yi jana’izar mahaifiyar tsohon gwamnan Jihar Legas, Alhaji Bola Ahmed Tinubu, wato Hajiya Habibat Magaji.  Tun daga lokacin ne…

A farkon wannan makon ne aka yi jana’izar mahaifiyar tsohon gwamnan Jihar Legas, Alhaji Bola Ahmed Tinubu, wato Hajiya Habibat Magaji.  
Tun daga lokacin ne ake ta tururuwa zuwa gidan tsohon gwamnan domin yi masa ta’aziyya. daya daga  cikin mutanen da suka je wa  tsohon gwamnan ta’aziyya shi ne tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, wanda ya taya Alhaji Bola Ahmed jimamin rashin da ya yi, wanda ya ce ba na  iyalan  tsohon gwamnan ba ne ko Jihar Legas kawai, na Najeriya gaba daya.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce marigayiyar ta yi  fice  wajen agaza wa  mai karamin karfi haka kuma ta shahara wajen inganta rayuwar mata da ma ’yan kasuwa, musammam  ma masu karamin karfi don haka ta bar gurbin da zai dauki lokaci mai tsawo kafin a samu wanda zai maye shi.
Alhaji Atiku ya sa an yi wa marigayiyar addu’a da fatan Allah Ya kara wa  tsohon gwamnan juriyar wannan rashin.
Shi ma tsohon gwamnan da yake wa bakon nasa bayanin yadda marigayiyar  ta rasu,  ya ce  ba shakka  ta  wuce ta bar shi da kewa kwarai da gaske.
Ya ce  hankalinsa kan  kara  tashi ne duk lokacin da ya shiga dakinta ya ga hotunanta da mutane iri daban-daban, daga masu hannu-da-shuni zuwa  masu karamin karfi.
Ita  dai Hajiya Habibatu Magaji ta rasu tana da shekaru 96 ne kuma daruruwan  jama’a ne suka yi dafifi  wajen yi mata rakiya, kana an rufe kasuwanni a duk fadin jihar domin yi mata addu’ar kwanaki 3 da rasuwa.