✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin sunan Tambuwal cikin ‘yan takarar gwamna ba abin damuwa ba ne – Dangwaggo

“Rashin ganin sunan Gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwa a jerin sunayen ‘yan takarar gwamna a PDP da hukumar zabe ta fitar a ranar Lahadin da…

“Rashin ganin sunan Gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwa a jerin sunayen ‘yan takarar gwamna a PDP da hukumar zabe ta fitar a ranar Lahadin da ta gabata ba wani abin damuwa ko tashin hankali da yin yamadidi ba ne, domin hukumar zabe ta sanar kowace jam’iya na iya canja dan takara ta sanya wanda take so daga nan har zuwa daya ga Disamba.”

Tsohon Shugaban APC a Sakkwato kuma jigo a PDP, Alhaji Muhammad Dangwaggo ne ya yi wadannan kalamai, a zantawarsa da Aminiya makon da ya gabata.

Dangwaggo ya kara da cewar “abin da ya baiwa PDP farin jini a Najeriya alkawalin da APC ta yi ne ya zama karya, da can matsalar Boko Haram ne kadai ake fama da ita, amma yanzu garkuwa da mutane ko’ina a dauke ka sai an sayar da gidanka da karo-karo a biya fansa, sannan a sake ka ka dawo kana haya. Amma duk tarihin mulkin PDP ba a kashe mutum 40 lokaci daya a yankinmu na Sakkwato ba sai a zamanin Buhari,” a cewarsa.

Ya ce Sakkwatawa na son Gwamna Tambuwal ne kan kokarinsa a harkar ilmi da lafiya da kulawa da matasa, mutanenmu suna da kawaici ba su son rashin kunya, tsohon gwamna guda ne aka jefa don ya kasa yarda da ikon Allah.

“Dan takarar PDP na shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar yana iya kayar da Buhari don yanzu kowa ya san shi da mutunci da son kasar nan, musamman a fannin tattalin arziki mutanen Najeriya sun gamsu da gogewarsa a sha’anin mulki,” in ji Dangwaggo.