✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Real Madrid ta dare saman teburin La Liga

Real Madrid ta haye saman teburin gasar La liga, bayan fafatawar mako na 21 ranar Asabar. Real ta samu wannan dama ce, bayan da ta…

Real Madrid ta haye saman teburin gasar La liga, bayan fafatawar mako na 21 ranar Asabar. Real ta samu wannan dama ce, bayan da ta ci Real Balladolid  daya mai ban haushi ta hannun Nacho Fernandez.

Hakan ya sa Real ta hada maki 46, inda ta yi nasara a karawa 13 da canjaras bakwai da rashin nasara daya. Kungiyar ta Santiago Bernabeu ta ci kwallo 39, sannan aka zura mata 13, zuwa wasan mako na 21.

Barcelona wadda ta dawo ta biyu da maki 43 ta ci karo da koma baya ne, bayan da Balencia ta doke ta  da ci 2-0.

Za a ci gaba da wasan mako na 22 a yau Juma’a, inda za a kece raini a tsakanin Billarreal da Osasuna.

Kawo yanzu Lionel Messi na Barcelona ne kan gaba a cin kwallo a gasar La Liga da kwallo 14.

Dan wasan Real Madrid, Karim Benzema ne ke biye da shi da kwallo 12.