✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Real Madrid za ta kara wa Cristiano Ronaldo albashin Naira biliyan 32

A yunkurin da kulob din Real Madrid da ke Sifen ke yi na jawo ra’ayin shahararren dan kwallonsa Cristiano Ronaldo na ganin bai canza sheka…

A yunkurin da kulob din Real Madrid da ke Sifen ke yi na jawo ra’ayin shahararren dan kwallonsa Cristiano Ronaldo na ganin bai canza sheka zuwa wani kulob ba, kulob din ya yanke shawarar sabunta kwantaraginsa da kuma kara masa albashi.
Bayanin haka na kunshe ne a lokacin da shugaban kulob din Florentino Perez yake ganawa da manema labarai a ranar Talatar da ta wuce.
Shugaban ya ce a kokarin karfafa wa dan kwallon gwiwa don ganin ya zauna  “tuni kulob din ya kammala shirye-shiryen kara wa dan kwallon tsawon kwantaragi zuwa shekarar 2018 da kuma yi masa kari a albashi.  A da kwantaragin dan kwallon za ta kare ne a shekaru biyu masu zuwa amma idan hakan ta tabbata yanzu kwantaragin zai kai shekarar 2018 kenan.”
Idan hakan ta faru, Cristiano Ronaldo zai kasance dan kwallon da ya fi kowane daukar albashi a duk fadin duniya.
A yarjejeniyar da ake sa ran kullata kafin a fara kakar wasa ta bana,  kulob din zai rika ba Ronaldo albashin Fam miliyan 20 bayan an cire haraji kwatankwacin Naira biliyan hudu a shekara har tsawon shekaru biyar masu zuwa.
Tun a shekarar bara ce Cristiano Ronaldo ya nemi kulob din ya kara masa albashi amma yanzu da kulob din ya ga take-takensa na neman barin kulob din ta sa ya amince da bukatarsa.
Cristiano Ronaldo, dan kimanin shekara 28 ya koma kulob din Madrid ne a shekarar 2009 daga kulob din Manchester United da ke Ingila. Ya zuwa yanzu ya zura kwallaye 201 daga cikin wasanni 199 da ya yi wa kulob din Real Madrid.
Tun lokacin da Ronaldo ya bayyana wa duniya ba ya jin dadin zama a Madrid a kakar wasan da ta gabata ce kungiyoyin kwallon kafa da dama da suka hada da Manchester United da Manchester City dukkaninsu da ke Ingila da kuma PSG da ke Faransa suka fara zawarcinsa da hakan ta sa aka fara rade-radin dan kwallon ya kusa barin kulob din.