Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Sakacin iyaye ke sa ana yi wa yaransu fyade – Hajiya Halima A. Aliyu

Sakacin iyaye ke sa ana yi wa yaransu fyade – Hajiya Halima A. Aliyu
Sakacin iyaye ke sa ana yi wa yaransu fyade – Hajiya Halima A. Aliyu

Hajiya Halima Asabe Aliyu tana daya daga cikin alkalai a Babbar Kotun Jihar Kebbi.   Ta kasance tsohuwar shugabar kungiyar Alkalai mata ta kasa da kasa (International Federation of Women Lawyers) (FIDA) reshen Jihar Kebbi, kuma tsohuwar shugabar kungiyar lauyoyi ta kasa (Nigerian Bar Association) reshen Jihar Kebbi. Sannan ta taba rike mukamin shugabar kungiyar fafutikar hakkin mata (Women’s Right Adbancement and Protection Alternatibe (WRAPA) reshen Jihar Kebbi, ta fito ne daga wani gari da ake kira Yauri a Jihar Kebbi. Mahaifinta tsohon ma’aikacin gwamnati ne ya rike mukamai da dama. Ta fara aiki ne tun daga matakin karamar lauya. A tattaunawarta da Aminiya ta tabo batutuwa da dama da suka shafi rayuwarta da ma wasu bangarori kamar haka:

 

ADVERTISEMENT

Tarihin Rayuwa:

Sunana Hajiya Halima Asabe Aliyu. An haifeni a Sakkwato a 1961.   Na fara  firamare a garin Minna a lokacin muna yankin Arewa maso Yamma, yanzu kuma tana Jihar Neja. Har na kai aji biyar daga bisani aka mayar da ni Sakkwato a can na kare firamare a 1972. Bayan na kammala firamaren a shekarar sai na shiga Kwalejin ’yan mata ta Gwamnatin tarayya (FGGC) Bauchi.   Mu muka bude makarantar.   Da na gama sai na tafi Kwalejin share fagen shiga jami’a da ke Kongo Zariya (School of Basic Studies), wanda haka ya ba ni damar samun gurbin karatu a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) ta Zariya, inda na karanci aikin lauya. Bayan na kammala sai na tafi makarantar horar da Lauyoyi da ke Legas a lokacin a Legas kadai ake da makarantar, bayan na kammala a 1986 zuwa1987 sai aka tura ni bautar kasa (NYSC) a Abuja.   Bayan na gama bautar kasa, sai na fara aiki a ma’aikatar jin koke-koken jama’a wato (Public Complain Commission) Abuja, lokacin an baro Legas an dawo Abuja, a wannan ma’aikata na bada gaggarumar gudummuwa, lokacin aiki yakan kai mu har wani lokaci saboda sabon ofis ne.

ADVERTISEMENT

Daga nan sai na koma ma’aikatar shari’a ta Jihar Sakkwato a matsayin karamar lauya, a 1991 da aka kirkiro Jihar Kebbi sai na koma ma’aikatar shari’a ta Jihar Kebbi, ina nan har na kai matsayin Darakta daga nan kuma sai na koma Abuja (Nigerian Law Reforms).

Bayan na shekara biyar a Abuja sai na koma Birnin Kebbi a matsayin Alkali ta babbar kotu da ke Jihar Kebbi, wanda yake yanzu ina a kan shi.

Ayyukan Kungiyar Mata Lauyoyi ta Fida:

Kungiya ce ta mata lauyoyi ba wai kawai iyakacin ta Najeriya ba, kungiya ce da kasashen duniya ke cikin ta. An kafa ta ne don taimakawa mata da kananan yara, muna kokari wajen ganin an ba mata hakkin su da Allah Ya ba su da kuma wanda kundin tsarin mulkin kasa ya tanadar musu a matsayinsu na mata. Muna kuma yaki da cin zarafin mata da kananan yara.

Ba wai muna yin fito na fito da maza ba ne, wajen karbar hakkin matan, don a wasu lokutan za ka samu mace ce take danne hakkin ’yar uwarta mace. Haka kuma a bangaren yara ana samun iyaye da kansu suna danne hakkin ’ya’yansu ta hanyar hana su zuwa makaranta da dora musu tallace-tallace ko irin iyayen da ke shaye-shaye. A wasu lokutan maza ma suna cin arzikin mata a wurin mu, domin a dalilin mace muna iya taimaka wa mijinta ko danta wanda yake babba, saboda mun yi imani cewa kwanciyar hankalin mace yana cikin kwanciyar hankalin iyalin ta. Idan mijin ta ko danta suka shiga matsala muna shigowa mu taimaka masa. A nan ka ga ya ci arzikin matarsa. Idan matan da ke da matsala sun sanar da kungiyarmu za mu tsaya musu don ganin sun fita daga wannan hali, mukan yi wa ma’aikata sulhu yadda za a samu nagartacciyar rayuwar iyali. Muna kuma tsayin daka ganin an hukunta masu yi wa kananan yara fyade da kuma cin zarafinsu.

Abin da take so a tuna ta da shi:

Ina son idan jama’a sun tashi tunawa da ni su ambace ni a matsayin matar da ta tsaya tsayin-daka wajen ganin an bai wa mai hakki, hakkinsa tare da tabbatar da adalci, ga jama’a musamman marasa gata.

Burin da take da shi:

Babban burina shi ne in cika da imani. Sannan ina da burin in ga cewa mai hakki an ba shi hakkinsa, sannan kuma a tabbatar da adalci a hukunci.

Yadda za a magance fyade a cikin al’umma:

Batun fyade ba wai yawa ya yi a yanzu ba, sai dai wayar da kai ake ta yi shi ne jama’a suke fitowa suke bayyana wa. Fyaden nan ba wai ya tsaya kan yara mata ba har ma maza, domin a yanzu zan iya cewa suna gogayya da juna.

A kullum ina fadin sakacin iyaye ne dalilin da ya sa ake yi wa yara fyade. Idan mun duba kullum muna gaya wa iyaye cewa masu fyaden nan ba baki ba ne.   Babu yadda za a yi bako ya zo unguwar ya yi fyade dole wanda ya san unguwa ne ko gidan. Lokutan da aka fi yin fyade nan mun san su kamar lokacin hantsi lokacin da magidanta sun tafi neman abinci su kuma yara masu dan girma sun tafi makaranta.

A wannan lokaci kuma yawancin mata suke kwanciya barci don hutawa. Su kuma kananan yara sai su fita waje don yin wasa daga nan sai a samu a yi musu fyade. Haka kuma lokacin tsakar rana iyaye mata suna can suna fama da harkar girki ba tare da sun sa ido a kan ya’ya’ynsu ba, haka kuma a wannan lokaci gari ya yi tsit shi kenan sai ka ga an dauki yara an yi musu fyade.

Haka kuma gab da magariba ma masu fyade na yin amfani da wannan lokaci wajen yin fyade. Don haka muke gaya wa iyaye su

kula da ’ya’yansu a wannan lokuta.

Haka kuma muna nuna wa iyaye su daina aiken yara da daddare idan ma aiken ya zama dole to a yi shi cikin gungun amma ba a aiki mutum daya ba.

Idan kuma har aka samu faruwar fyade, wanda ba ma fata, kada a wanke komai, a yi hanzarin kai yaran asibiti, kuma akwai bukatar iyaye su jajirce har sai sun kwato wa ’ya’yansu hkkinsu a gaban shari’a, wannan shi zai sa wadanda suke yi da kuma wadanda ke da niyya su ji tsoro, su bari.

Shawara ga mata:

Ina shawartar ’yan’uwana mata su jajirce wajen neman abin kanmu fiye da maza. Saboda ita mace ita ce madubin da ’ya’yanta ke dubawa. Idan uwa ta zama marar zuciya za ka ga ’ya’yanta ba  za su yi wani abin kirki ba, koda kuwa ya kasance mahifinsu mai zuciyar nema ne kuma Allah ya kawo mu wani zamani maza ne ke mutuwa suna barin mu da ’ya’ya, idan kina neman na kanki ko da Allah ya yi wa maigida rasuwa za ki iya tattala abin da ya bari, koma bai bari ba ke kanki kina da dan abin da kike juya wa a hannunki, za ki samu don za ki iya kula da iyalinki da iliminsu da sauransu.

Sannan ina shawartar uwa da ta zama tagari mai gaskiya a cikin dukkannin lamurranta. Akwai bukatar kuma ta nemi ilimi, lallai kada mace ta zauna da jahilci na fannin addini da kuma na rayuwa. Su rika yin hakuri a rayuwa, su rika bin komai sannu a hankali, su rika neman shawarwari a duk lokacin da wani abu ya shige musu duhu. Su rika yin biyayya ga na-gaba. Su rika sanya tsoron Allah da yin gaskiya a rayuwa. Idan suka rike wadannan abubuwa ko shakka babu za su samu nasara a rayuwa.

Kuma iyaye su rika hana ’ya’yansu mata kanana rike wayar hannu domin akwai illa da kuma kallon fina-finai na banza wadanda ba su da amfani.   Haka maza masu dukan matansu, suna wulakanta su, suna cin mutuncin su, su ji tsoron Allah, su tuna fa da ’ya’ya da mata kiwo ne Allah Ya ba su, idan sun danne hakkin su, Allah Zai tambaye su gobe kiyama.

Kasashen da na je:

Na je Dubai da Saudi Arebiya ba sau daya ba.  Na je Ghana da Nijar. Zuwa na Dubai aiki ne ya kai ni na taron kungiyar lauyoyi na kasa da kasa, wanda na jagoranci mata lauyoyi zuwa wurin taron. Haka ma a Ghana, mun je taro ne na sati guda don mu kara koyon yadda ake yin sulhu a tsakanin jama’a ba tare da an kai mutum kotu ba.

Kyawawan halayen maigidana:

Gaskiya maigidana yana da halaye masu kyau. Duk da dai ko a tsakanin harshe da hakori akan saba, amma a gaskiya bai taba bata mini rai ba.

Hasalima yana mutunta ni, yana kula da ni, yana ba ni hakki daidai gwargwado kafin Allah Ya yi masa rasuwa. Allah ya gafarta masa, amin.