Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Sanatoci sun yi wa Emefiele fatan samun nasara a karo na biyu

Bayan tantance gwamnan babban bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele a yau Laraba a matsayin shugaban bankin CBN a karo na biyu. `Yan malisar dattawan sun yi wa Emefiele fatan alheri kuma sun ce, sun gamsu da ayyukan shi da ya yi a baya.

Gwamnan CBN ya yi kimanin mintuna 20 ya na yi wa kwamitin tantancewar bayanin nasarori da kalubalen da ya fuskanta tun lokacin da yake jagorantar bankin daga watan Yuni 2014 zuwa yanzu. `Yan sun gamsu da yadda Gwamnan ya kawo hanyoyin da ya bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

ADVERTISEMENT