✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarakuna sun nemi a dakatar da Oluwo na Iwo daga mulki

Dattawa sun yi zanga-zangar lumana kan fadan da ya kaure tsakanin Sarki da Hakimi Sarakuna 15 daga kananan hukumomin Ayedire da Ola-Oluwa a Jihar Osun…

  • Dattawa sun yi zanga-zangar lumana kan fadan da ya kaure tsakanin Sarki da Hakimi

Sarakuna 15 daga kananan hukumomin Ayedire da Ola-Oluwa a Jihar Osun sun nemi Gwamna Gboyega Oyetola, ya hanzarta dakatar da Oluwo na Iwo, Oba Abdulrasheed Adewale Akanbi daga mulki bisa dalilin abin kunyar da suka ce ya aikata a ranar Juma’ar da ta gabata inda ya kama daya daga cikinsu wato Agbowu na Ogbaagba Oba Dhikrulahi Akinropo da duka a bainar jama’a.

Sarakunan sun yi wannan kira ne a wata takardar koke da suka rattaba wa hannu suka mika wa mahukuntan jihar a ranar Litinin da ta gabata.

Sun nemi Gwamnan ya dakatar da Oluwo daga matsayinsa na Shugaban Majalisar Sarakunan Iwo. Kuma sun bukaci ’yan sanda su kammala bincikensu domin gurfanar da Oluwo a gaban kotu a kan wannan lamari da suka ce, ya tozarta sarautar gargajiya da zubar da kimarta. Sarakunan sun ce, “Ya kamata Gwamna Oyetola ya dauki matakin gaggawa a kan Oluwo na Iwo, domin ba ma son ganin ’yan daba dauke da makamai suna ziyartar fadarmu.”

A safiyar ranar Litinin dattawan garin Ogbaagba sun yi zanga-zangar lumana a ofishin Gwamnan da ke Osogbo inda suka nemi mahukunta su dakatar da Oluwo daga mulki dalilin dukan da ya yi wa sarkinsu Agbowu na Ogbaagba Oba Dhikrulahi Akinropo.

Masu zanga-zangar suna rike da kwalaye dauke da rubutu masu  cewa: “Gwamna Oyetola ka cece mu” da “Oluwo ya wulakanta al’ada” da “A hanzarta dakatar da Oluwo daga karaga” da “Wajibi ne a yi adalci.”

Bayanin da gwamnati ta yi a ranar ta nuna rashin jin dadinta da aukuwar lamarin, inda ta ce, “Gwamnati tana sane da matakin shawo kan matsalar da Majalisar Sarakunan Jihar ta dauka. Muna fata majalisar za ta bi kyakkyawar hanyar samar da zama lafiya a tsakanin sarakunan jihar domin ba ma bukatar hargitsi a ko’ina a Jihar Osun.”

Kwamishinar Watsa Labarai ta Jihar, Uwargida Funke Egbemode, ce ta rattaba hannu a takardar sanarwar.

Aminiya ta jiyo cewa, a ranar Juma’ar jiya ne fada ya kaure a tsakanin Oluwo na Iwo, Oba Abdulrasheed Adewale Akanbi da hakiminsa Agbowu na Ogbaagba Oba Dhikrulahi Akinropo, inda Sarkin ya kama hakimin da duka a gaban mahalarta wani taron sulhu da Mataimakin Sufeto Janar Mai Kula da Shiyya ta 11, Alhaji Bashir Makama ya yi da sarakunan a ofishinsa da ke Osogbo hedkwatar Jihar Osun.

Bayanai sun ce, Mataimakin Sufeto Janar Bashir Makama ne ya raba fadan tsakanin sarkin da hakimin wanda ya samu rauni a fuskarsa, kuma aka kai shi Babban Asibitin Gwamnati na Asubiaro da ke Osogbo, domin yi masa magani. Ofishin Mataimakin Sufeto Janar din ya gayyaci Oluwo na Iwo da dukkan hakimansa ne zuwa taro ne domin sulhuntawa a kan zargin da Oluwo yake yi wa hakiman na sayar da filaye mallakarsa a cikin hurumin masarautarsa ba tare da izninsa ba.

A ranar Juma’a da al’amarin ya auku daya daga cikin hakiman da suka halarci sulhun, Olu na Ile Ogbo, Oba Habeeb Agbaje Adetoyese, ya yi wa ’yan jarida bayanin cewa, “A bara ne Oluwo ya aika da rubutacciyar takarda ga mahukunta yana zargin wadansu daga cikinmu da sayar da filaye mallakarsa. Hakan ya sa Gwamna ya gayyace mu zuwa taron sulhu na farko a ofishinsa, inda Oluwo ya hargitsa taron. Dalili ke nan da gwamnati ta umarce mu da sake halartar sulhu a Ofishin Mataimakin Sufeto Janar da muka yi (a ranar Juma’a), inda Oluwo, ya ambaci sunan mutum uku; Olu na Ile Ogbo da Agbowu na Ogbagba da Onigege na Igege, cewa mu ne muke sayar da filaye mallakarsa ba tare da izninsa ba,” inji shi.

Ya ce “Oluwo bai gamsu da bayanin da na yi a gaban taron ba  cewa, ban sayar da wani fili mallakarsa ba amma na sayar da fili ne mallakar Masarautar Ile Ogbo, wanda a nan take Oluwo ya tashi a fusace ya dumfari Agbowu na Ogbaagba ya rika naushinsa a kansa, Agbowu ya fadi kasa, muka kai shi asibiti.”

Da yammacin ranar ce Oluwo na Iwo Oba Abdulrasheed Akanbi, ya bayar da sanarwa da ya rattabawa hannu inda ya ce, “Yaya za a yi kurtun dan sanda ya ci mutuncin kwamishinansa da barazanar dukansa? Akwai wani Sarki ko hakimi da ya isa ya yi wa Ooni na Ife ko Alaafin na Oyo irin wannan?”

Ya ci gaba da cewa, “Wadannan hakimai sun hada kai ne domin nuna kiyayya ga dokokin Masarautar Oluwo, wadda ita ce ta nada su bisa mukaman da suke kai a yanzu.” Ya ce, a wajen taron ne Agbowu na Ogbaagba, ya rika kiran shi (Oluwo) da sunan mahaukaci da yunkurin dukansa da sandar sarauta a fuska bayan dakatar da shi daga bayanin da yake yi a gaban taron.

Shi kuwa Agbowu na Ogbaagba Oba Dhikrulahi Akinropo, wanda ya samu rauni a fuskarsa a wajen taron sulhun cewa ya yi, zai kai karar Oluwo ne a kotu kan wannan lamari. Cikin bayanin da lauyansa Mista Babajide Siyanbola ya yi, ya ce ba za su taba kyale wannan cin mutunci da aka yi wa Agbowu ba, ba tare da neman bi masa hakki ba.