✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarrafa Albarkatun Gona: Tafarnuwa

Zan fara duba harkar saye da sayar da tafarnuwa a kasuwanninmu na gida da na waje a cikin jerin makalun sarrafa albarkatun gona da nake…

Zan fara duba harkar saye da sayar da tafarnuwa a kasuwanninmu na gida da na waje a cikin jerin makalun sarrafa albarkatun gona da nake gabatar wa masu karatu a wannan filin. Tafarnuwa na daya daga cikin kayan abinci da magunguna da aka fi amfani da su gaba daya a duniya. Kusan kowane jinsi na duniya na amfani da tafarnuwa, musamman wanda ke zaune a kasashen da ke cikin Hamada da makwabtansu, da kuma kasashe masu sanyi. A Najeriya, musamman ma a arewacin Arewa, ana amfani da tafarwanuwa wajen maganin cututtuka da sanyi ke haifarwa, da kuma kariyar jiki daga irin wadannan cututtuka. Saboda mahimmancinta ga al’umma, tana da daraja kwarai a kasuwannin duniya.
   Masana ilmin magunguna a duniya sun hakakance sun kuma tabbatar da ingancin tafarnuwa a matsayin sinadarin da ke inganta lafiyar  dan Adam. Sun ce tafarnuwa na gyara zuciya da habaka garkuwar jiki da ba jiki kariya mai mahimmancin gaske. Tafarnuwa na kuma taimakawa kwarai da gaske wajen zagayawar jini a jikin mai amfani da ita. Sannan kuma tafarnuwa ta fi kowane tsiro dauke da wani sinadari a cikinta da ake kira ‘Germanium’da Turanci, wanda ke yaki da cutar daji (ko Cancer da Turanci). Tafarnuwa kuma na maganin tsiron jiki (ko tumor da Turanci), ta kuma saukar da hawan jini, ko hana jinin hawa, tana kuma daidaita yawan sigan da ke cikin jini ta kashe tsutsar ciki, ta kone man da ke jikin mutum da ka iya jawo masa hawan jini ko shanyewar jiki .
   Wata hanya kuma da tafarnuwa ke amfanar mutane ita ce, wadata jiki da sinadarin bitamins na ajin ‘A’da na ajin ‘B’da na ajin’B2’ da na ajin ‘C’; sai kuma sinadarin  ‘Calcium’ da sa karfin kashi da hakora, da kuma sinadarin ‘Zinc’ da sauran sinadarai masu amfani a jiki. dimbin amfanin tafarnuwa ya sanya ta ta shahara a duniya, wanda hakan ya sa ake neman ta, ya kuma kasance ko’ina ma kasuwarta ce.
Ana samun tafarnuwa a jihohin arewacin Najeriya, musamman ma Kano da Kaduna  da Bauchi da Sakkwato da Barno da Jihar Kebbi. Najeriya na daya daga cikin kasashe masu noma tafarnuwa a duniya da kuma sayar da ita, inda kasar Amurka ke kan gaba wajen noma da kuma sayenta, domin wacce kasar ke nomawa ba ta isar bukatarta. asar Sifen ce kasar da ta fi sayar da tafarnuwa a duniya. Sauran kasashen da suka yi suna a kasuwar tafarnuwa a duniya sun hada da kksar Meziko da Masar da Bulgeriya da Japan da Romaniya da Poland da Faransa da Indiya. kasashen da kuma ke kan gaba wajen tafarnuwa a duniya sun hada da Amurka da Kanada da kasashen da ke Tarayyar Turai.     
    Zan yi bayani a kan iri-iren tafarnuwa da ake samu a kasashen duniya, musamman ma a gida Najeriya, tare da darajar su, idan Sarki Allah Ya kai mu makon gobe. Zan kuma yi wa dan kusuwa mai niyyar shiga harkar saye da sayar da tafarnuwa, walau a gida Najeriya ko a kasashen waje, bayanin yadda zai sarrafata domin samun alherin da ke cikin harkar.