Da Dumi Dumi

Shaguna 16 sun kone a tsohuwar kasuwar Sakkwato

‘Yan kasuwa sun tafka hasara a gobarar da ta shi a tsohuwar kasuwar Sakkwato, inda a ranar Litinin da ta gabata wuta ta tashi kuma akalla ta kone shaguna 16 da ke  Layin Zama’u.

Wadansu da lamarin ya faru a kan idonsu sun ce wutar ta fara ne da misalin karfe 11, kuma ta yi awa uku tana ci kafin jami’an kashe gobara su zo su kashe ta.

Shugaban ’Yan kasuwar Alhaji Mustafa ya nuna damuwarsa kan faruwar lamarin lokacin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce an yi asarar kaya na miliyoyin Naira, amma ya yaba wa jami’an kashe gobara kan daukin gaggawa da suka kai.

Alhaji Mustafa yana cikin wadanda lamarin ya rutsa da su ya ce shaguna 16 ne suka kone da ake sayar da shinkafa da man girki da wasu kayan abinci.

Ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Sakkwato ta taimaka musu kan irin aasarar da suka yi domin da wannan kasuwanci ne suke ciyar da iyalansu.

ADVERTISEMENT

Shugaban sashen kula da kashe gobara a hukumar kashe gobara ta jihar, Alhaji Mustafa Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce za su yi bincike don sanin musabbabin wutar.

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya aika sakon jaje ga ’yan kasuwar ta hannun Mataimakinsa Maniru Muhammad Dan’iya, sannan ya yi kira da jami’an tsaro su kula da inda lamarin ya faru kada batagari su yi awon gaba da kayan jama’a.

Share