✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa: Ina mafita?

ALHAJI IBRAHIM AHMAD KATSINA shi ne Shugaban Gidauniyar Peace Builders Security Council (Gidauniyar Samar da Dauwamammen Zaman Lafiya da Tsaro da Zamantakewar Al’umma). Ya kasance…

ALHAJI IBRAHIM AHMAD KATSINA shi ne Shugaban Gidauniyar Peace Builders Security Council (Gidauniyar Samar da Dauwamammen Zaman Lafiya da Tsaro da Zamantakewar Al’umma). Ya kasance Babban Bako Mai jawabi a yayin taron Kungiyar Gizago ta Kasa da aka gudanar a Katsina a ranar Asabar (22-09-2018), inda ya gabatar da wannan takarda dangane da illolin tu’ammali da miyagun kwayoyi:

Tsokaci:

“Matasa ne kashin bayan ci gaban kowace al’umma. Idan aka kula da su a yau, za a samar da ingantacciyar al’umma a nan gaba kuma idan aka banzatar da su, aka kyale su sasakai, to babu shakka nan gaba al’umma za ta girbi mummunan sakamako…”

“Hanya mafi sauki da za a bi a lalata kowace irin al’umma, ita ce ta hanyar jefa matasa cikin shaye-shayen miyagun kwayoyi… idan suka siffatu da shaye-shaye, za su kasance gurbatattu, lalatattu, su jefar da neman ilimi, ba za su iya tsinana wa kansu komai ba a rayuwa, inda daga karshe kuma za su kasance bayin dillalan kwaya.”

“A kiyayi shan kwaya, domin kuwa tu’ammali da miyagun kwayoyi kan ingiza mutum cikin tunanin cewa yana cikin Aljanna, alhali cikin jahannama yake.”

Gabatarwa:

Babu shakka, matasa su ne kashin bayan ci gaban kowace irin al’umma, don haka abu ne mai muhimmanci a kula da rayuwarsu da jin dadinsu, wanda nauyin haka ya dogara kacokan ga gwamnatin da ta san abin da take yi.

A wannan zamani da muke ciki, al’umma na fuskantar wani al’amari mai ta da hankali, wanda ke gabatar da babbar barazana ga zaman lafiyar kasa, kuma ke barazana ga ci gaban matasa da na al’umma baki daya. Wannan al’amari shi ne na batun shaye-shaye da tu’ammali da miyagun kwayoyi da sauran nau’o’in kayan maye ya zama yayi musamman ga matasa. Wannan matsala ta zama tamkar ciwon daji da ke zagwanyar da rayukan matasa, wadda muddin ba a dauki matakin taka mata birki ba, to lallai za ta ruguza al’ummarmu a nan gaba. Abin takaicin ma shi ne, matasanmu da suka yi fice a wannan harka, suna daukar ta tamkar wani abin yayi, abin burgewa a tsakanin kininsu, ta yadda ba su ankara da illar da ke tattare da al’amarin sai wuri ya kure.

Wani abin takaici ma shi ne, shugabannin al’umma ba su mai da hankali ga matsalar ba, an zuba ido tana cin karenta babu babbaka, an kasa la’akari da irin hadarin da ke tattare da ita wadda ka iya ruguza al’ummarmu mai zuwa nan gaba. Wani shiri da kafar labarai ta BBC ta gabatar a kwanakin baya game da yawaitar tu’ammali da miyagun kwayoyi musamman a Arewa, ya kamata ya zama darasin da zai sanya mu farka daga dogon barcin da muke yi, domin mu tunkari matsalar tun kafin dare ya yi mana.

A shekarar 2012, Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta samu sahihan bayanai game da yadda ake tu’ammali da miyagun kwayoyi a makarantun kasar nan, ta kuma samu irin wadannan bayanai daga asibitoci na adadin mutanen da suke jinyar cutar da ke da nasaba da shaye-shaye; ta kuma samu bayanan da aka nada daga bakunan mutanen da hukumomi suka kama dangane da laifuffukan da suka shafi tu’ammali da miyagun kwayoyi. Sakamakon da aka samu daga wadannan bayanai ya nuna cewa matasa ne ke da kashi 90 cikin 100 na laifin safara da shan miyagun kwayoyi da kayan maye a kasar nan. Wannan abin firgici ne da tsoratarwa ga rayuwar matasanmu kuma abin taka-tsantsan ne ga gwamnati da al’umma, wanda muddin ba a dauki matakin magance shi ba, to kuwa zai salwantar da rayuwar matasanmu, kuma zai raunata ci gaban kasarmu a nan gaba. Duk da cewa dokokin Najeriya sun halatta tu’ammali da giya da sigari a wani adadi, sai dai kuma addinanmu da al’adunmu sun kyamace su ko sun haramta su gaba daya. Haka, an samu bayanin da ke cewa giya da sigari tamkar kofa ce da ke jagorantar mutum zuwa ga tu’ammali da miyagun kayan maye da suka hada da tabar wiwi, Hodar Iblis (heroin) da koken. Kamar yadda marubuci Cole (2014) ya bayyana: “Shaye-shaye da tu’ammali da miyagun kwayoyi na haddasa cututtuka da matsaloli masu yawa ga al’ummarmu. Irin wadannan cututtuka sun hada da hauka, sankarar huhu, yayin da kuma matsalolin suka hada da kaurace wa makaranta da yadda matasa kan rasa rayukansu tun a kuruciyarsu sakamakon shaye-shaye.”

Lallai al’ummarmu tana cikin tsaka-mai-wuya, domin  tu’ammali da miyagun kwayoyi a bayyane yake baro-baro, inda za ka ga matasa, har ma da wadansu tsofaffi suna afawa, da nufin samun kuzari ko don su huce wani takaici ko kuma don su mance da wani bakin ciki da ke gallabarsu. Wadansu kuma suna shan kwaya ne da nufin su fitar da tsoro ko don su yi maganin kadaici, wanda idan ba sun sha kwayar ba, ba za su samu wannan biyan bukata ba. Irin wadannan mutane ne ke shan kwaya domin aiwatar da miyagun ayyukan siyasa, musamman tsoratar da abokan adawa ko su yi “maganin” wadanda suka dauka abokan gabarsu. Da kadan-kadan suke fara sha har abin ya zame musu jiki, inda a can gaba kuma sai su zama alakakai, ka ga sun fada cikin gungun manyan ’yan ta’adda – wannan abin takaici ne!

Ma’anar tu’ammali da kwaya

Tun asali, ita kwaya magani ce da ake amfani da ita wajen magance cututtukan da kan addabi jikin mutum. A ganin wani masani mai suna Caroll (1989), kwaya na nufin wani sinadari, wanda da zarar ya shiga jikin mutum zai canja fasalin aikin jikin da tsarin gudanarwarsa. Don haka ma’anar tu’ammali da kwaya na nufin sha, yin allura ko zukar hayakin duk wani sinadari ba da izinin likita ba, ko kuma amfani da wani magani ba da nufin magance wata cuta ba, inji Ibrahim (2016).

Ma’anar sabo da kwaya:

A lokacin da mutum ya kasance ba zai iya rayuwa ba tare da ya sha wani sinadari ba, to za a iya cewa ya kamu da cutar shan kwaya, wadda haka na faruwa ne sakamakon jimawa a cikin shan magani ba da izinin likita ba, ko ba da nufin magance wata cuta ba. Idan an shiga wannan yanayin, ke nan an samu yanayin da zai haifar da matsalar mutum ya kasa barin sha da kuma sauran matsaloli da kan iya kawo masa cikas cikin al’umma, a wurin aiki ko a makaranta, kamar yadda masani Akus (2010) ya fada. Akalla dai a nan, ana nufin sabo da kwaya shi ne mutum ya dogara da shan wani magani ko sinadari duk tsawon rayuwarsa.

 

Za mu ci gaba