✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 20 da kafuwa: Kamfanin FKD zai karrama ’yan fim

Kamfanin Shirya Fina-Finai na FKD, mallakar jarumi Ali Nuhu ya shirya karrama ’yan fim da suka taimaka wajen daga martabar kamfanin nasa tun kafuwarsa a…

Kamfanin Shirya Fina-Finai na FKD, mallakar jarumi Ali Nuhu ya shirya karrama ’yan fim da suka taimaka wajen daga martabar kamfanin nasa tun kafuwarsa a shekarar 2000, shekara 20 da suka gabata.

Kamfanin ya shirya fina-finai da dama, da suka tabo bangarorin rayuwa da daban-daban, sannan ya fitar da jarumai da dama da a yanzu ake damawa da su a masana’antar.

Fim din farko na kamfanin shi ne Sabani da aka fitar a watan Janairun 2000, sai na karshe zuwa yanzu shi ne Bana Bakwai.

Ali Nuhu ya rika sanya tsakure daga cikin wasu fina-finan kamfaninsa na FKD, inda yake rubuta shekara 20 na kamfanin FKD.

Domin murnar cika shekara 20 da kafuwar kamfanin, kamfanin na FKD tare da Dandalin Masoya Ali Nuhu, (Ali Nuhu Fans Club) suka shirya domin gudanar da bikin karrama wadansu ’yan fim da suka taimaka wajen taka rawa a bangarori da dama wajen gina kamfanin.

A wata sanarwa da Ali Nuhu ya saka, wanda ya kalato daga shafin na masoyansa a Instagram, cewa aka yi, “Wannan dalili ya sa Kamfanin FKD Production tare da Dandalin Masoya Ali Nuhu wato @ali_nuhu_fans_club suka shirya wani gangamin biki da ake sa ran zai hada ’ya’yan wannan masana’anta domin taya wannan kamfani murna. Tare Kuma da bada kambin karramawa ga wadansu daga cikin wadanda suka taka rawa a bangarori daban-daban wajen gina wannan kamfani har zuwa wannan lokaci.”