✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Aljeriya na samun turjiya kan neman tazarce

Shugaban Kasar Aljeriya mai shekara 82 Abdelaziz Bouteflika da yake fama da shanyewar rabin jiki shekara shida da suka gabata kuma yake da wahalar gaske…

Shugaban Kasar Aljeriya mai shekara 82 Abdelaziz Bouteflika da yake fama da shanyewar rabin jiki shekara shida da suka gabata kuma yake da wahalar gaske ya yi tafiya ko magana yana samun turjiya kan tazarcen da yake nema domin ya ci gaba da mulki karo na biyar.

An sanar cewa Shugaba Abdelaziz Bouteflika zai yi takara domin neman wa’adi na biyar, amma ba a gan shi ya fito ba domin ya yi rajistar neman takarar.

Tuni dalibai da malamai da kuma lauyoyi a kasar suka fara fitowa kan titi suna gudanar da zanga-zangar adawa da yunkurin, inda suka fito karara suka nuna cewa ba su yarda Shugaban da ba a gane kansa ba ya ci gaba da jagorantar kasar.

Mutane da dama a kasar sun damu cewa rashin samun wanda zai gaji Shugaba Bouteflika da ya hau mulki a 1999 zai iya kasancewa an samu matsala a kasar idan har ya rasu a gadon mulki.

Jawabin karshe da Shugaban ya gabatar ya yi shi ne a shekarar 2014 lokacin da ya yi jawabin godiya ga  al’ummar kasar Aljeriya bayan sake zabensa a matsayin Shugaban Kasa.

Ya bayyana shirye-shiryensa domin kara karfin bangaren zartarwa da na shari’a da na dokoki da kuma duba irin rawar da bangaren adawa ke takawa da bayar da tabbacin ’yanci ga mutanen kasar kamar yadda gidan rediyon BBC ya rawaito.

Mutanen kasar sun hangi Shugaban a talabijin lokacin da yake gaisawa da wadansu baki daga kasashen waje. Kuma sun gan shi a wani taro da aka yi a shekarar 2016 a talabijin inda aka nuno shi a kan keken guragu. Amma sai a 2018 aka gane cewa jam’iyyarsa tana kokarin sake tsayar da shi takarar shugabancin kasar.

Bayan makonni kadan, an zagaya da Shugaban domin duba aikin gina wani babban masallaci a birnin Aljes wanda zai lashe  kimanin Dala biliyan 2, kuma shi ne masallacin da zai zamo na uku a girma a duniya.

Har yanzu Shugaban ba ya da abokin karawa da zai zamo barazana gare shi ganin cewa tun a 2014, Shugaban ya lashe zaben da aka yi ba tare da ya yi wani kwakkwaran yakin neman zabe ba.

A tarihin siyasar kasar, jam’iyyar adawa a kasar kanta ya rabu.

Jam’iyya mai mulki a kasar wato FLN ta mulki kasar tun lokacin da kasar ta samu ’yancin kanta a 1962 bayan wani yakin da aka kwashe shekara bakwai ana zubar da jini.

’Yan siyasar kasar da suka hada da wadansu daga cikin ’yan adawa da wadanda suka mulki kasar ta hanyar hadaka tsakaninsu ko kuma suka ja ragamar gwamnatin na shekaru da dama suna shan suka daga wurin jama’ar kasar.

BBC ya rawaito wani shahararren marubuci na kasar Aljeriya Kamel Daoud yana shaida wa wata jaridar Faransanci cewa manyan kasar suna sace hakkokin matasan kasar. Ya ce kawo dan takara wanda ya kusan mutuwa a halin yanzu alamar raini ce ga matasan kasar wadanda a yanzu haka kusan kashi 30 cikin 100 na ’yan kasar da ke kasa da shekara 30 ba su da aikin yi.

Ba za mu bari rikici ya barke ba- Rundunar soji

A nasa bangaren, Hafsan Hafsoshin Sojin Aljeriya Janar Ahmad Gaid Salah ya ce sojojin kasar ba za su bari rikicin siyasar kasar ya yi kazancewar da ya yi a 1999 ba. A wancan lokaci rikicin siyasar kasar ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutanen kasar dubu 200. Janar Ahmad Gaid Salah na wadannan kalamai ne bayan zanga-zangar da ta barke a manyan biranen kasar da masu adawa da tsawaita wa’adin mulkin Shugaba Bouteflika ke yi.

Wadannan jerin zanga-zangar sun fara ne kwana 11 da suka gabata kuma babu alamar za a daina zanga-zangar nan kusa. Masu zanga-zangar suna cewa sun gaji da mulkinsa kuma suna neman ganin an kawo karshen rashin aikin yi da cin hanci da rashawa a kasar.