Daily Trust Aminiya - Shugaban PDP na Kano ya koma APC
Subscribe

Shugaban PDP na Kano ya koma APC

Shugaban Jam’iyyar PDP na Kano, Rabiu Sulaiman Bichi ya bar Jam’iyyar PDP ya koma Jam’iyyar APC mai mulki.

Bichi ya tabbatarwa kafar Premium Times cewa zai fitar da bayani game da batun ficewarsa daga jam’iyyar.

Rabiu Bichi tsohon na hannun daman Kwankwaso ne da suka dade suna tare, inda ya yi aiki da Kwankwaso a matakai daban-daban.

Bichi ne koma Jam’iyyar APC ne kwana biyu bayan Kotun Koli ta tabbatar da zaben Gwamna Ganduje.

A zaben da ya gabata, Rabiu Bichi ne babban wakilin Jam’iyyar PDP a zaben gwamna da Shugaban Kasa.

texem
More Stories