Search
Subscribe
Shugabancin Majalisa: PDP ta goyi bayan Ali Ndume da Umar Bago

Shugabancin Majalisa: PDP ta goyi bayan Ali Ndume da Umar Bago

Kwamitin gudanarwa na jam’iyyyar adawa ta PDP ta ce, bayan ta kammala tattaunawa da masu fada aji na jam’iyyar sun amince da goyon bayan Sanata Ali Ndume a matsayin shugaban majalisar Dattawan Najeriya tare da Umar Mohammed Bago a matsayin Kakakin majalsar Wakilan Najeriya, wanda ake saran rantsar da su a yau Talata.

Sakataren jam’iyyar PDP na kasa Sanata Umar Ibrahim Tsauri, ne ya sanar da hakan a yau Talata, inda ya ce sun amince da wannan goyon bayan ne sakamakon ganawar da suka yi da jigogin jam’iyyar.

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin