Shugabannin addini sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Iseyin

Limamin Iseyin yana sanya hannu a kan yarjejeniyar
Limamin Iseyin yana sanya hannu a kan yarjejeniyar

Shugabannin addinan Musulunci da Kirista da addinin gargajiya a garin Iseyin a Jihar Oyo sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya a lokutan bikin al’ada na ‘Oro’ na bana da mabiya addinin gargajiya suka fara yi a ranar Asabar da ta gabata, inda za su shafe kwana 17 suna yi.

An kulla yarjejeniyar ce a gaban mahukunta a hedkwatar ‘yan sanda da ke Eleyele a Ibadan.

Kwamishinan ’Yan sanda  Mista Shina Olukolu ne ya kira taron masu ruwa-da-tsaki don tattaunawa kan lamarin saboda kauce wa rikicin da aka yi a bara a irin  wannan lokaci wanda ya haifar da hasarar kadarori da munanan raunuka a garin Iseyin.

Mahalarta taron sun tattauna kan bikin al’ada na bana da mabiya addinin gargajiya suke yi a kowace shekara inda suke lullube jikin dodannin Oro da kyallaye suna kade-kade da raye-raye da wakokin gargajiya suna yawo a hanyoyi domin kai gaisuwar ban girma ga Sarki, wato Aseyin na Iseyin a fadarsa tare da ziyartar wuraren al’ada.

A lokacin da dodannin Oro suka fito kan hanya, addininsu bai yarda su yi ido biyu da mata ba. Su ma sauran mutane suna kebe kawunansu cikin gidaje ne a wasu lokuta da ake bikin.

ADVERTISEMENT

Al’ummar Musulmi a garin  Iseyin ne suka fara kai korafi ga mahukunta inda suka nuna rashin amincewa kan yadda bikin na Oro yake takura wa rayuwarsu musamman lokacin ibadarsu da hana mata da ’ya’yansu fitowa domin gudanar da harkoki ko zuwa makaranta da hana jama’a gudanar da kasuwanci na wani lokaci tare da amfani da wannan dama da wadansu ke yi wajen tayar da hankalin jama’a da sata da ke haifar da takaddama a tsakanin Musulmi da mabiya addinin gargajiya a garin.

Hakan ne ya sa Kwamishinan ’Yan sanda Shina Olukolu, ya kira taron wanda ya samu halartar Aseyin na Iseyin Oba Abdulganiyu Salaudeen da mai ba Gwamna shawara a kan harkokin tsaro tsohon Kwamishinan ’Yan sanda Fatai Owoseni da Babban Limamin Iseyin Sheikh Abdulhakeem Olajori da Shugaban Kungiyar Kiristoci (CAN) reshen Iseyin Rabaran Christopher Olugbade da jagoran mabiya addinin gargajiya Oloye Fadare Famiyi da kwamishinoni biyu da masu ba Gwamna shawara. Taron ya yanke shawarar cewa, ranar farko da Dodon Oro zai fito da rana ta 2 da ta 3 su ne ranaku masu muhimmanci a tsawon kwana 17 na bikin. Saboda haka aka amince da fitowar dodon da karfe 5:30 na safe a ranar farko da karfe 5:30 na yamma a rana ta 2 da ranar karshe.

Kafin shugabannin addinan su sanya hannu kan yarjejeniyar sai da kowannensu ya yi bayanin amincewa a gaban taron domin guje wa aukuwar rikici a lokacin bikin da bayansa. Dukkansu sun yi kira ga mabiya addinin gargajiya su tabbatar cewa, sun kebe hanyoyin da dodanninsu za su rika ratsawa a cikin gari domin kauce wa takura wa jama’a.

Kwamishinan ’Yan sandan ya nemi masu shirya bikin su gudanar da bukukuwan a tsanake domin doka za ta hukunta duk wanda aka kama da laifin tayar da zaun- tsaye. Wakilan gwamnati sun tunatar da al’ummar garin Iseyin kan muhimmancin zaman lafiya wanda zai kawo ci gabansu kuma rashin haka zai kai ga karkatar da ayyukan ci gaba zuwa wani yanki maimakon yankinsu.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya