✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojin Syria sun kwace garin Maaret al-Numan bayan hare-haren bam 

  Dakarun Gwamnatin Syria sun kwace wani gari mai muhimmanci da ke hannun ’yan tawaye a yankin Arewa maso Yammancin kasar bayan kai hare-hare daga…

 

Dakarun Gwamnatin Syria sun kwace wani gari mai muhimmanci da ke hannun ’yan tawaye a yankin Arewa maso Yammancin kasar bayan kai hare-hare daga sojin Rasha – wadanda suka tilasta dubban daruruwan mutane gujewa daga garin zuwa tuddan-mun-tsira.

Maaret al-Numan, wanda a baya ya shahara  a matsayin garin da aka yi ta gudanar da zanga-zangar nuna kin jinin gwamantin Bashar al-Assad – yanzu ya zama kango bayan da aka share watanni ana jefa bama-bamai a cikin garin da ke tsakanin biranen Aleppo da Damaskus babban birnin kasar.

“Cikin kwanakin nan, dakarunmu sun samu nasarar fatattakar ’yan tawaye daga kauyuka da garuruwa da daman gaske, ciki har da Maaret al-Numan,” inji wani kakakin sojin kasar cikin wani jawabi da aka yada ta talabijin, shekaranjiya Laraba.

“Sojojin yanzu sun mayar da hankali kan “farautar dukkan kungiyoyin ’yan tawayen da ke rike da makamai, har sai an share dukkan wani na’uin ta’addanci a kasar Syria,” inji shi.

A shekarar 2011, garin Maaret al-Numan ya zama daga cikin wadanda suka fara yi wa gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad bore a Lardin Idlib, kuma shekara daya bayan haka, ’yan tawaye masu yakar gwamantin suka kwace iko da garin.