Daily Trust Aminiya - Ta ware tukuicin Naira miliyan 2.5, ta yi hayar jirgin sama
Subscribe

Ta ware tukuicin Naira miliyan 2.5, ta yi hayar jirgin sama don gano karenta da aka sace

Wata mata mai suna Emilie Talermo, ta ce za ta yi duk abin da za ta iya don gano inda karenta mai shekara biyar yake bayan sace shi da aka yi.

Emilie ’yar birnin San Francisco ta ware Dalar Amurka dubu 7000 (kimanin Naira miliyan 2 da dubu 530 da 500, a matsayin tukuici ga wanda ya gano karenta, kuma ta dauki hayar jirgin sama da zai taimaka wajen neman inda karen yake a birnin. Karen jinsin karnukan kasar Austireliya ne da aka sace a wani shagon sayar da kayan abinci a karshen mako.

Jirgin saman zai ci karin Dalar Amurka 1,200 (kimanin Naira dubu 433 da 800, kuma za a  sanya sanarwar neman karen da aka sace mai  Jackson a gefen shagon sayar da kayan abinci da ke makwabtaka da gidan wanda ta mallaki karen.

Emilie Talermo, ta fadi a ranar Alhamis  din makon jiya cewa“Zan yi duk abin da zan iya don ganin an gano inda karena yake, ina bukatar taimako kan yadda za a gano inda karena  yake.”

Wani hoton bidiyo ya nuna wani mutum yana kusantar karen da ke daure a wani benci a gefen shagon sayar da kayan.

Emilie da kawayenta sun rabar da dubban takardu da ke dauke da hoton karen mai nauyin kilo 13 mai launin fari da baki a jikinsa a matsayin cigiya.

Emilie, ta kaddamar da shafin Intanet mai taken: www.bringjacksonhome.com, inda ta bayyana kebe Naira miliyan 2 da dubu 530 da 500, a matsayin tukuici. Ta kuma bude asusun ajiyar kudi na banki ga karen nata da aka sace.

Ta ce, “Wannan karen a koyaushe ina tare da shi, ina kaunarsa matuka, sannan ina neman taimakon gano karen matuka.”

Emilie, ta yi hayar jirgin saman dauke da tambarin da ke nuna ana cigiyar karen nata da aka sace tare da adireshinta na San Francisco da Oakland na kusan awa biyu a ranar Juma’ar da ta gabata. Da farko an shirya cewa, jirgin zai tashi a ranar Alhamis ne amma saboda sauyin yanayi aka canja zuwa Juma’a.

Don samun taimakon wasu kungiyoyi, Emilie ta kaddamar da gidauniya ta musamman mai suna ‘GoFundMe’ inda ta tara kudin da suka kai sama da Naira miliyan 2 da dubu 530 da 500. Kuma tana shirin mika sauran kudin ga gidan taimakon karnuka na Rocket Dog Rescue.

Emilie, ta ce ta sayi karen ne mai shekara biyar a Jihar New York da ke Amurka sannan suka wuce Los Angeles daga bisani suka tafi San Francisco. “Duk wadanda suka san ni sun san irin soyayyar da nake yi wa karen,” inji Emilie.

texem
More Stories