Da Dumi Dumi

Ta’aziyyar Jaruman Kannywood: Abin da ’yan kannywood suke cewa

Marigayi Bashir Liman (a baya) tare da Darakta Kamal Alkali da Fati Washa da Nafisa Abdullahi da sauran ’yan fim din Hausa lokacin daukar wani fim
Marigayi Bashir Liman (a baya) tare da Darakta Kamal Alkali da Fati Washa da Nafisa Abdullahi da sauran ’yan fim din Hausa lokacin daukar wani fim

Na shiga uku – Rahama Sadau

Rahama Sadau ta wallafa a shafinta na Instagram, tana cewa, “Innalillahi wa inna ilaihirraji’una. Allah Ya jikanka da rahama, Bashir Liman. Allah Ya sa Aljanna ta zamo makoma a gare ka. Na shiga uku, lallai wannan duniyar ba komai ba ce. Ya kamata mu koyi son juna.”

Allah Ya yi maka rahama – Ali Nuhu

Shi ma Sarki Ali Nuhu cewa ya yi, “Allah Ya jikanka, Bashir Liman, Ya yi maka rahama alfarmar Manzon Allah.”

Mun yi rashin masoyi – Abdul Amart

ADVERTISEMENT

Furudosa, Abdul Amart Maikwashewa cewa ya yi, “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Awa uku da suka wuce ya kira ni. Kannywood mun yi rashin masoyi mai kishinta. Allah Ya yafe maka, Bashir.

Mutumin kirki ya rasu – Hadiza Gabon

Ita ma Hadiza Gabon ta sanya sakon muryar da ya aike mata ne, sannan ta ce “Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Ya kasance mutumin kirki.”

Sauran wadanda suka yi ta’aziyyarsa sun hada da Fati Shu’uma da Darakta Kamal S Alkali da Abdul M. Shareef da A’ishatu Humaira da Uzee Usman da Bello Mohammed Bello da sauransu, inda duk suna nuna babban rashin da suka yi.

 

Share