✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takaddama ta barke a kan gawa a Kalaba

Takaddama ta barke a tsakanin al’ummar Musulmi mazauna Kalaba  da iyalan Mista James da ke Kalaba sakamakon rasuwar Suleiman James, bayan ya sha fama da…

Takaddama ta barke a tsakanin al’ummar Musulmi mazauna Kalaba  da iyalan Mista James da ke Kalaba sakamakon rasuwar Suleiman James, bayan ya sha fama da jinya na wasu kwanaki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Kalaba a ranar Asabar din makon jiya. Kafin rasuwar Suleiman James, dan kasuwa ne mai sayen tsofaffin karafa yana sayarwa, kuma dan siyasa da ke shugabancin Jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Kalaba ta Kudu kuma jigon jam’iyyar a bangaren ’yan Arewa mazauna Kalaba.

Musulmi mazauna Kalaba da ke kasuwanci tare da marigayi Suleiman James, sun yi sakaci ba su ajiye wani Musulmi ya rika kula da shi lokacin da yake jinya ba, sai ’yan uwansa da ba Musulmi  ba ne suke jinyarsa a asibitin, don haka lokacin da ya rasu sai Musulmi abokan kasuwancinsa da suke yi tare a Layin Bagobiri a Unguwar Hausawa suka zo kan gawarsa za su dauke ta su yi mata sutura, inda ’yan uwan mamacin suka ce, fastoci ba za su bari Musulmi su dauki gawar ba, suka ce nasu ne ya riga ya bar Musulunci.

Rigima har gaban Sarkin Hausawa Alhaji Salisu Abba Lawan wanda ya tabbatar wa ’yan uwan marigayin cewa ba su da hakki a kan gawar marigayi ta Musulmi ce, su bari a yi masa jana’iza a binne shi, amma sai suka ki, inda har zuwa aiko wannan rahoto gawar tana can a ajiye a dakin ajiye gawa na haya da ’yan uwan marigayin suka bayar a ajiye kafin a gama takaddamar.  An ajiye ranar Asabar da ta gabata kan za a hadu da ’yan uwan marigayin da wakilan Musulmin a gaban Sarkin Hausawa amma ’yan uwan ba su zo ba.

Daga bisani Aminiya ta tuntubi Malam Ahmad Bassey, Limamin Masallacin Karamar Hukumar Birnin Kalaba wanda dan asalin Jihar Kuros Riba ne, kamar marigayi Suleiman, inda ya ce, “Wannan ja-in-ja da ake yi a ka’ida kowane dan asalin Kudancin Najeriya ya Musulunta kamar yadda mu muke yi a nan Kuros Riba za ka rubuta takarda cewa, ka Musulunta koda ta Allah ta kasance Musulmi ne za a ba su gawarka su yi maka sutura kada ’yan uwanka da kowa su taba maka gawa, kuma idan mutum yana da lauya zai rubuta masa shi ma duk sai mutum ya bi ’yan uwa bangaren uwa da uba ya ba su a rubuce mai yiwuwa shi marigayin bai yi haka ba shi ya sa ake ta wannan ja-in-ja.”

Wani malamin addini ya shaida wa Aminiya cewa, “Musulunci addini ne mai sauki idan ’yan uwan sun ki bayar da gawarsa, to sai Musulmi su yi masa Sallar Gawa ta Ga’ibi wato a yi Sallar a roka masa rahama kamar yadda addini da shari’a suka tanada, a kyale su domin idan aka biye musu babu mamaki abin ya kawo rikici.”