✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambaya da Amsa: Sakonnin tes daga masu karatu (7)

Tambaya: Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya tare da iyalanka, allahumma amin. Ni ma’abocin karanta kasidarka ce a shafukanka da dama. A halin…

Tambaya: Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya tare da iyalanka, allahumma amin. Ni ma’abocin karanta kasidarka ce a shafukanka da dama. A halin yanzu ina da takardar shaidar gama sakandare kuma ina sha’awar karatun kwamfuta ta zamo ita ce ta gaba, duk da  ba ni da wata masaniya game da kwamfuta a aikace, sai dai a karance, ta hanyar kasidunka da nake karantawa. Wannan dalili ya sa nake neman shawara daga gare ka da ta ina ya kamata in fara?                   Ni ne dalibinka Amiru Usman daga Lafiya Jihar Nasarawa.

Amsa: Wa alaikumus salam, Malam Amiru Usman.  Na yi farin ciki da jin irin tasirin da wannan shafi namu ya yi a kanka wajen zaburar da kai don neman karin ilimi a wannan fage mai matukar tasiri a duniyar yau.  Shawarata ita ce, akwai makarantu ko wuraren horar da masu sha’awa a wannan fanni, a aikace, wato: “Computer Training Centers” ke nan. A wadannan wurare kana iya yin ‘Certificate’ ko “Diploma” a fannin kuma a aikace. Ma’ana kafin ka gama, za ka iya sarrafa kwamfuta wajen kunnawa da kashewa da yin rubutu da lissafi da zane da kuma yadda ake taskance bayanai da fitar da su ta hanyar na’urar buga bayanai, wato “Printer.”

Halartar wannan cibiya zai taimaka maka ta bangare biyu. Bangaren farko shi ne, za ka samu kwarewa a aikace, tare da shaidar gama karatu. Bangare na biyu kuma za ka samu karin sha’awa da son abin a zuciyarka. Idan kana ganin ba ka san komai ba ne, sai ka je wurin za ka ga wadanda ka fi su. Da zarar ka samu wannan kwarewa, ba sai na gaya maka abin da za ka yi nan gaba ba. Tuni za ka samu shawarwari daga wajen malaman da suka koyar da ku.

Wannan ita ce shawarata gare ka. Fanni ne da ke bukatar aikata abin da aka koya ko aka karanta. Nazari a takarda kadai ba ya isarwa ko gamsar da dalibi. Ina yi maka fatan alheri a duk inda ka samu kanka, tare da rokon Allah Ya ba ka juriya da jajircewa a wannan fage. Da fatan ka gamsu.

Tambaya: Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya amin. A baya na yi maka tambaya amma ba ka amsa ba. To ga ni tafe da wata tambayar. A kasidunka da ka yi bayani game da yadda za a koyi ilimin gina manhajar kwamfuta wato “Programing,” ka ce sai mutum yana da wata kwarewa ta sarrafa kwamfuta kafin ya kai kansa ga koyon wannan bangare. Sai dai ba ka fadi wata irin kwarewar da ta kamata a ce mutum ya samu kafin ya fara koyon ba. Kuma, mutumin da yake da kwarewar da ake samu a makarantun nan nakan titi zai iya aukawa ga koyon wannan bangare ko kuma akwai matakin da ya kamata mutum ya kai kafin ya kai kansa ga koyon wannan bangare na programming?                                              Ka huta lafiya, dalibinka Amiru Usman.

Amsa: Wa alaikumus salam Malam Amiru. Lallai watakila ba ka ci karo da cikakken jawabin da na bai wa mai tambayar ba. Na tabbatar da cewa dole sai ka iya sarrafa kwamfuta, wajen kunnawa da kashewa da iya rubutu a kai tare da sanin yadda ake sarrafa ta tukun.  Auka wa ilimin “Programming” ba tare da sanin yadda ake iya sarrafa kwamfuta ba, zai zama tsallen badake. Kamar mutum ne bai iya tuka mota ba, amma ya yi rajista a makarantar tseren motoci. Ka ga ganganci ne wannan, kuma babu wata fa’ida da za a iya samu, sai ma cutarwa.

Dangane da tambayarka ta biyu cewa ko mutum na iya wadatuwa da irin horarwar da ake samu a makarantun kwamfuta na kan titi, amsar ita ce, eh. Muddin ka san yadda ake sarrafa kwamfuta da yadda take aiki, musamman yadda ake shigar mata da bayanai da yadda ake nemo su, babu laifi. Bayanin yaya za a yi mutum ya fara wannan karatu kuwa yana cikin jawabin tambayarka ta farko, wacce ke saman wannan amsar.  Da fatan ka gamsu, kuma Allah Ya sa a dace, amin summa amin.  Na gode.

Tambaya: Salamun alaikum, barka da himma Baban Sadik; gaisuwar girmamawa dangane da shafinka na Kimiyya da Kere-Kere. Wallahi ni dai kai ne ka ja hankalina na jibinci karanta Aminiya saboda jin dadin bayananka masu ilimantarwa. Ina godiya. Allah Ya kara fasaha kuma da fatan ka yi Sallah lafiya.                                                        Daga M. Bashir Zariya.

Amsa: Wa alaikumus salam Malam M. Bashir, ina yi maka fatan alheri, tare da jin dadi musamman ganin cewa wannan shafi ya yi tasiri a rayuwarka wajen sanya ka cikin karatun jaridar Aminiya. Ina rokon Allah Ya kara maka himma da jajircewa da kuma basira don fahimtar abin da kake karantawa. Na kuma gode da addu’o’inka gaba daya. Allah Ya saka maka da alheri, amin.

Tambaya: Assalam da fatan an wuni kalau, Malam. Daya daga cikin mabiya filin kimiyya a jaridar Aminiya ne ke tafe da wata bukata. Bukatar kuwa ita ce, ina neman shawara game da aiki da ake yi a yanar gizo, wanda akan yi a samu kudi wato Freelance. Na samu nasarar rajista a freelancer.com<http://freelancer.com/> a fannin Graphics Design, amma daga bisani suka bukaci in biya kimanin Dala biyar ($5) ta Mastercard dina. Malam don Allah ina neman karin haske.                                                                      Lukman Suleiman Abbas daga Maiduguri.

Amsa: Wa alaikumus salam, Malam Lukman barka ka dai.  Tsarin “Freelancing” hanya ce ta yin aiki ta hanyar Intanet, ba tare da haduwa da abokan huldarka ba kuma a biya ka kudinka bayan ka gama aikin da aka ba ka. Hanya ce da ke bukatar kwarewa a wani fanni na musamman. Akwai gidajen yanar sadarwa a Intanet da dama da ke bayar da wannan dama, tun da zai yi wahala a ce kowa ya mallaki shafinsa don tallata kwarewarsa ga duniya. Ire-iren wadannan shafuka ne suka ba ka dama ka yi rajista, don tallata kwarewarka a ilimin zanen-hotunan kwamfuta. Shafin freelancer.com na daga cikin shahararru a Intanet.

Dangane da bukatar da suka yi cewa sai ka biya Dalar Amurka biyar  ($5) kuma, wannan ladar hidimar da suka yi maka ne, wadda ta kunshi ba ka damar yin rajista, da hakan zai sa masu bukatar kwarewarka su same ka kai-tsaye, ba matsala. Bayan wannan, za ka rika amfani da manhajojin da suka tanada ne a shafinsu wajen musayar bayanai a tsakaninka da wadanda za su bukaci kwarewarka nan gaba. Wannan kuwa, kamar yadda za ka gani, hidima ce mai girma da suke yi wa mutane irinka, kuma yana bukatar kudaden tafiyar da shafin gaba daya, wanda daga ire-iren wadannan hanyoyi ne suke tarawa.

Don haka, idan ka samu natsuwa da kuma gamsuwa da tsarin muhallin da cewa yin rajista ko biyan kudin rajistar zai ba ka damar haduwa da abokan cikini ne nan gaba da za su iya ba ka aiki har ka samu kudaden shiga, kana iya amfani da katinka na ATM don biyan kimar wannan kudi, wato Dala 5.  Idan kuma ba ka gamsu ba, kana iya bari. Amma ka sani, biyan kudin zai taimaka wajen bayyana ka ne, tare da tallata ka ga dimbin masu hawa shafin ne don neman masu kwarewa daban-daban.

Wannan shi ne dan gajeren bayanin da zan iya yi maka dangane da wannan tsari. Ina yi maka fatan alheri da dacewa cikin abin da ka sa a gaba na alheri. Kuma da fatan ka gamsu. Na gode.

Tambaya: Assalamu alaikum, da fatan Malam ya wuni lafiya, Allah Ya kara mana ilimi da basira. Don Allah Malam a taimaka mini da takaitaccen bayani a kan Blogging da kuma Web Hosting.

Amsa: Wa alaikumus salam, barka dai. Kalmar “Blogging” tana ishara ce ga manhaja da ke dauke da tsarin taskance bayanai a shafukan Intanet, musamman ra’ayoyinka kan harkokin rayuwa. Wadansu kwararru kan fassara kalmar da “Taskar Intanet” ko kuma “Mudauwana.”  Duk dai kokari ne na ganin an bayyana hakikanin abin da manhajar ta kunsa. Akwai shafukan Intanet da dama da ke bayar da damar yin rajistar Taska a Intanet, kyauta. Shahararru daga cikinsu su ne “Wordpress” (<http://www.wordpress.org>) da kuma “Blogger” (<http://www.blogger.com>) wanda kamfanin Google ya mallaka. A farkon lamari, kamar shekara goma da suka shude, kwararru a fagen sadarwa da aikin watsa labaru (kamar ’yan jarida) ne kadai suke amfani da wannan tsari ko manhaja wajen isar da ra’ayoyinsu ga duniya. Amma a halin yanzu an samu ci gaba, ta inda kamfanonin kasuwanci da hukumomin gwamnatocin kasashen duniya suka shiga cikin harkar tsundum su ma, domin isar da sakonni kan abin da ya shafi manufofinsu na kasuwanci ko makamantan haka.

A daya bangaren kuma, kalmar “Hosting” na ishara ne ga tsarin taskance bayanai da shafukan Intanet, don bai wa masu ziyara damar isa gare su, a wata kwamfuta ta musamman da ke iya mika su ga kwamfutocin da suka bukata. Wannan kalma tana da alaka ta kai-tsaye da fannin ginawa da tsara gidan yanar sadarwa, wato “Web Design.” Duk wani gidan yanar sadarwa idan aka gama gina shi, karshensa na karewa ne a tumbin wata kwamfuta da za ta rika mika wa masu ziyara duk shafin da suka bukata, ta hanyar adireshin da ke zunguro shafin kai-tsaye ko a kaikaice. Akwai kamfanonin da ke adana shafukan Intanet a duniya da dama, don bai wa masu ziyara damar isa ga bayanan. Shahararru daga cikinsu su ne, “Hostgator” (<http://www.hostgator.com>) da kuma “GoDaddy” (<http://www.godaddy.co.uk>).

Wannan shi ne bayani a takaice kan ma’anonin kalmomin guda biyu. Don neman karin bayani, kana iya ziyartar wadannan shafuka da na kawo don ganin abin a aikace, a misalce. Da fata an gamsu. Na gode.

Tambaya: Salamun alaikum Abban Sadik.  Don Allah ni ba ni da waya babba balle in ce a tura mini kasidun ta Imel. Ina bukatar kasidar Tsibirin Bamuda ne, don Allah a buga min a jarida ni ma in karanta.

Amsa: Wa alaikumus salam, barka dai. Tabbas an buga kasidar Tsibirin Bamuda a wannan shafi har sau biyu. Kuma ganin cewa kasida ce mai tsayi, kuma ta maimaitu a wannan shafi mai albarka, ina iya cewa ma tana cikin kasidun da suka fi sauran shahara a tsakanin masu karatu, na sanya dokar tsayar da sake buga ta a wannan shafi na jarida. Sai dai idan mai karatu na da adireshin Imel, ko kuma yana da wayar salula mai iya hawa Intanet, sai ya garzaya zuwa babbar Taskar Baban Sadik da ke: <http://www.babansadik.com> don samun damar karantawa ko ma saukar da kasidar kai-tsaye, ba tare da matsala ba.

Don haka, idan kana da wayar salula mai amfani da kwamfuta, ba dole sai kana da Imel ba, kana iya zuwa wancan shafi namu, inda nake taskance dukan kasidun da aka taba buga su a wannan shafi, shekara 10 da suka gabata ko ma 11, don fa’idantuwa da duk abin da kake sha’awa na ilimi. Da fatan za a gafarce ni kan wannan doka. Allah sa a dace, amin.