✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambayoyi da sakonnin masu karatu ta imel da tes (6)

Assalamu alaikum Baban Sadik, yaya aiki?  Allah ya taimaka, amin. Don Allah ina son a taimaka a turo mini da kasidar nan ta Bamuda Triangle…

Assalamu alaikum Baban Sadik, yaya aiki?  Allah ya taimaka, amin. Don Allah ina son a taimaka a turo mini da kasidar nan ta Bamuda Triangle ta wannan adireshin: [email protected].  Na gode.  Ibrahim Kabir Bakori: 08107110505

 

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Ibrahim. Kamar yadda na sha sanarwa, akwai gidan yanar sadarwar da na bude inda nake taskance dukkan kasidun da nake rubutawa a wannan shafi mai albarka. Kana iya ziyartar wannan shafi don samun dukkan makalar da kake bukata, muddin na taba rubutu a kai. Ga adireshin kamar haka: https://www.babansadik.com/category/teku.  Idan ka bi wannan rariyar likau, za a riskar da kai ne kai tsaye ga bangaren da ke dauke da makalolin da suka shafi Teku, wanda makalar Tsibirin Bamuda na daga cikin makalolin da ke wannan bangare.  Sai ka bisu daya bayan daya, za ka ci karo da ita. Allah sa a dace, Ya kuma amfanar damu abin da muke karantawa ko rubutawa, amin. Na gode.

Assalamu alaikum Baban Sadik, ina fatan kana lafiya.  Allah ya kara daukaka da basira. Dan Allah a taimaka a yi min bayani a kan shafin Facebook dina.  Idan na jima ban yi amfani dashi ba, duk lokacin da na hau na sa lamba da kalmar sirri, sai a ce na manta kalmar sirrin.  Sai su turo min wata, da zarar na sa sai kawai inga ya bude.  Amma kuma idan na sake hawa na sa wannan da suka turo min sai ta ki budewa.  Dan Allah a yi min bayanin wannan matsala.

Daga Bashiru Musa Kura: 08105283189.

 

Wa alaikumus salam Malam Bashir, barka ka dai. Ina godiya da tarin addu’o’inku gareni.  Allah albarkacemu baki daya, amin.   Bayani kan matsalar da kake samu, ina iya cewa matsalar daga gareka take.  Tsawon lokacin da kake dauka baka hau ba ke sa ka mance kalmar sirrinka, wato: “Password”.  Shi yasa da zarar ka sa, sai ace ba daidai yake ba.

Lambobin da ake aiko maka ba su bane “Password” dinka.  Ga alama kana matsa inda aka ce: “Forget Your Password?”, sai a kai ka inda za ka bukaci a aiko maka da lambobin tantancewa, wanda suke aiko maka ta layin wayarka ko imel dinka.

Wannan wata hanya ce ta musamman da hukumar Facebook ta tanada don taimaka wa masu mance kalmominsu na sirri ko wadanda wasu suka musu kutse a shafukansu, don samun damar sabunta kalmar sirri.

Shi ya sa da zarar ka shigar da lambobin nan take sai a bude maka.  Asali ya kamata a kai ka shafin da za ka sake zaban sabuwar kalmar sirri ne, wato: “New Password”.  Watakila baka lura ba, ko kuma an zarce da kai ne kai tsaye, domin tsare-tsarensu kan canja lokaci-lokaci.

Don haka, lambobin da aka aiko maka ka shigar na wannan lokacin ne kadai.  Aikinsu ba ya wuce mintuna 15.  Wannan yasa da zarar ka zo hawa a lokaci na gaba, ka shigar da su, sai ace maka ba daidai bane.  Aikinsu ya kare.

Abin da za ka yi yanzu shi ne, ka koma shafinka, ka shigar da lambar waya ko sunan da ka saba shigarwa, sannan ka latsa inda aka rubuta: “Forget Your Password?” ko wani abu makamancin haka.  Idan aka zarce da kai inda ake neman ka bukaci a aiko maka lambobin tantancewa, sai ka latsa.  Da zarar an aiko maka lambobin, sai ka shigar.  Shafi zai budo, za ka ga an rubuta: “Add New Password”, a kasa kuma an sa: “Retype New Password”.

Wurin farko ana so ne ka zabi sabuwar kalmar sirri.  A wuri na biyu kuma ana so ne ka maimaita kalmar da ka zaba, don tabbatar da cewa lallai kai dan adam ne, ba wata na’ura bace.  Kana gama haka shike nan.  Nan gaba idan ka zo hawa, sai kayi amfani da sabuwar kalmar sirrin da ka zaba.  Za a baka kofar shiga kai tsaye.

Da fatan ka gamsu.  Allah sa a dace, amin.

Salamun alaikum Baban Sadik. Da fatan an yi hidimar Sallah lafiya. Dan Allah na bude shafi a dandalin Facebook, yanzu ba na bukatarsa. Yaya zan yi in rufe shi?

Daga Aminu Ado.

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Aminu.  Ai wannan abu ne mai sauki, wai cire wando ta ka.  Kawai ka hau shafinka, idan a wayar salula kake hawa, sai kaje bangaren “Settings” sai ka gangara bangaren “Pribacy”, ka shiga wajen.  Shafi zai bude, inda za ka ga zabi guda biyu.  Na farko “Deactibate Account”.  Idan ka zabi wannan tsari za a kulle shafin na wani lokaci kawai.  A duk sadda ka ga dama ka sake hawa, shafin zai dawo da dukkan bayananka.  Na biyu kuma shi “Delete Account”.  Wannan tsarin idan ka zabe shi, za a rufe shafin ne, sannan a goge shi gaba daya, bayan makonni biyu.  Idan makonni biyu ba su gama cika ba ka dawo ka hau, za a tambayeka ko kana son ci gaba da tafiyar da shafin ne?  Idan ka ce eh, sai a zarce da kai.  Amma idan ka ce a a, za a wullar da kai waje, a sake kulle shafin.  Da fatan ka gamsu.

Allah sa a dace, amin.