✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tanko Almakura da Abdullahi Adamu sun yi nasara a zaben Sanata

  Gwamnan jihar Nasarawa, Umaru Tanko Almakura da tsohon gwamnan jihar Sanata Abdullahi Adamu , dukkansu na jam’iyyar APC sun yi nasara a zaben majalisar…

 

Gwamnan jihar Nasarawa, Umaru Tanko Almakura da tsohon gwamnan jihar Sanata Abdullahi Adamu , dukkansu na jam’iyyar APC sun yi nasara a zaben majalisar dattawan jihar.

Baturen zaben yankin Farfesa Ahmed Yakubu Ashuku ya ce Tanko Almakura ya samu kuri’a 113,156 yayi da abokin hamayyarsa na PDP, Sulaiman Adokwe ya samu kuri’a 104,595.

Kazalika Sanaa Abdullahi Adamu ya samu kuri’a 115,298 yayin da abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Bala Ahmed Aliyu, ya samu kuri’a 85,615 kamar yadda rahoton BBC ya nuna.