✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi Babi na Talatin da Bakwai:-

Babi na Talatin da Bakwai:- Idan mutum ya yi wa wani kyautar godiya to ya kasance kamar mai bayar da umra da sadaka. Wasu mutane…

Babi na Talatin da Bakwai:-

Idan mutum ya yi wa wani kyautar godiya to ya kasance kamar mai bayar da umra da sadaka. Wasu mutane sun ce, “Yana iya amshe (fasawa) cikinta.”
345. An karbo daga Humaid ya ce: “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, “Na ji Malik yana tambayar Zaid dan Aslam sai ya ce: “Na ji Babana yana cewa: Umar (Allah Ya yarda da shi) ya ce, “Na taba daukar nauyin wani mutum bisa kyautar wata godiya sai na gan shi zai sayar da ita,. Sai na tambayi Manzon Allah (SAW) game da haka sai ya ce: “Kada ka saye shi kuma kada ka koma karbar sadakarka.”

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai.
Littafin Bayanin Shaidu.
Babi Na Farko:-
Abin da ya zo game da bayanin kawo shaida ga mai kara. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ya ku wadanda suka yi imani idan za ku bayar da bashi a tsakaninku zuwa wani ajali sananne to ku rubuta…har zuwa karshen aya (2:282).” Da fadarsa cewa: “Ya ku wadanda suka yi imani, ku kasance masu adalci kuma masu shaidawa domin Allah….har zuwa karshen fadarsa cewa: Shi game da abin da kuke aikatawa Masani ne zai ba ku labari (4:135).”

Babi Na Biyu:-
Idan mai bayar da shaida akan wani ya ce: “Ba mu sani komai ba game da shi face alheri, ko ya ce, “ban san komi ba game da shi face alheri.” Sai Imamu Bukhari ya koro hadisin kazafi bisa fadar Annabi (SAW) ga Usamat lokacin da ya nemi shawararsa ya ce: “Rike iyalinka ba mu san wani abu ba tare da ita face alheri.”

346. An karbo daga Hajjaju ya ce: “Abdullahi dan Umar Annamiri ya ba mu labari ya ce, Thababan ya ba mu labari ya ce, “Laisu ya ce, Yunus ya ba ni labari daga dan Shihab ya ce, Urwat da dan Musayyab sun ba ni labari da Alkamat dan Wakkas da Ubaidullahi dan Abdullahi daga hadisin (labarin) A’ishat (Allah Ya yarda da ita), sashen wasu hadisan su na gaskata sashe lokacin da mutane masu kazafi suka fadi abin da suka ce, game da ita. Sai Manzon Alah (SAW) ya kira Aliyu da Usamat lokacin da wahayi ya yi jinkiri yana mai neman shawararsu cikin rabuwa da iyalinsa. Amma Usamat sai ya ce: “Rike iyalinka ba mu san komai ba game da ita face alheri.” Barira ta ce: “Babu wani abin da zan zargeta da shi face dai ita yarinya ce mai karamin shekaru takan yi barci ta bar garin iyalinta har awaki su su ci.” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wane ne zai taimake ni wajen daukar fansa bisa ga wanda zai cutar da iyalan gidana? Ina rantsuwa da Allah ban san komai ba game da iyalina face alheri. Lallai sun ambaci (zargi) wani mutum wanda ban san komai akansa ba face alheri.”