✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taron Makomar kasa?

Kwamitin da Shugaban kasa Jonathan ya kaddamar wanda zai shimfida hanyoyin da za a bi a ga an samar da zama na musamman dangane da…

Kwamitin da Shugaban kasa Jonathan ya kaddamar wanda zai shimfida hanyoyin da za a bi a ga an samar da zama na musamman dangane da makomar kasar nan abu ne da zan iya kiransa ihu bayan hari ko kuma babarodo. Dalilina na farko dai shi ne kwamitin da taron da zai shirya da matsayar da taron za ta assasa wa kasar, ba abubuwa ne da ke boye ba, an riga an san matsalolin kasar, tattauna su ba magani ba ne, domin kuwa mai ciwon ya san maganin da zai warkar da shi. Ke nan kamar a ci mutane da yaki ne daga baya su hau ihu, bayan an gama barna. Dalili na biyu shi ne taron zai iya zama babarodo, ganin cewa dukkan matsayar da za a cimmawa a wurin taron, sai kuma an sake kai ta ga ’yan majalisar kasa sun sa albarka, sun amince, sun daidaita, sa’annan a soma amfani da ita domin ciyar da kasar gaba.
Ke nan idan mutum ya natsu sai ya ga cewa ina amfanin kafa kwamitin da kuma yin taron da samar da matsayar da kila ba za a taba aiwatar da ita ba? Ina amfanin badi ba rai, tun da ba rayuwar za a yi ba? Mene ne amfanin barnatar da dukiyar kasa don yin taron da bai zai samar da makomar da ake bukata ba?
kila wani ya ce me ya sa zan yi wadannan tambayoyi. Mu yi wa kanmu hisabi. Tun da farko abin da aka ce shi ne ’yan Najeriya sun kasa zama tsintsiya madaurinki daya, yawancin al’ummar kasar ba-sa-ga-maciji da junan su. Mutanen Arewa na dardar da mutanen Kudu. A cikin na Arewar, na tsakiyar Najeriya na cewa su ba ’yan Arewa ba ne. A can cikin mutanen Kudu, na Yammaci na shakkun mutanen Gabas. Mutanen Gabas na ganin mutanen Kudu-maso-Kudu a matsayin wadanda ba za su iya amincewa da su ba. Ke nan kawunan al’ummar kasar ya rarrabu, saboda haka ana bukatar a samar da taro don daidaita makomar wadannan gantalallun al’umma.
Wani dalilin da ake bayarwa na dole a tattauna makomar kasar nan shi ne ballagazar siyasar kasar. Kudu na mulki, ba ta son ta ba Arewa. Ita kuma Arewa ta dana, ta ji dadi, ta rasa, yanzu kuma tana son mulkin ya sake dawowa hannunta. Su kuma ’yan tsiraru na cewa ai sun gaji da mulkin danniyar manyan yankunan kasar, abin da suke bukata shi ne a bar kanana su dana su ma, kananan kuwa daga Kudu da kuma Arewa.
Wani dalilin kuma da ake bayarwa na son gudanar da taron kasar shi ne bambance-bambancen addini. Wasu na ganin cewa dole ne Kirista ya ci gaba da mulki, su kuma Musulmi na cewa ai su ya dace a ba mulkin kasar, su kuma wadanda ba su da addini na ganin cewa su ba a yi da su, saboda haka ya dace a ba su dama su ma.
Idan mutum ya natsu ya yi nazarin wasu daga cikin irin wadannan korafe-korafe da ake ta yi, wadanda su ne suka ingiza ake neman a tattauna makomar kasar, sai mutum ya ga cewa ba gaskiya ake son a yi ba. Dukka ko yawancin wadannan matsaloli za a ga cewa ba abin da ya jawo su face rashin adalci da tsari ko shirmantaccen shugabanci. Haka kuma ba wasu ne suka dasa wadannan mataloli ba face su wadannan mutane da ake son su  zauna a tebura su samar wa kasar makomar da ta dace. Ke nan tamkar abin nan da Hausawa ke cewa an ba Kura kiwon Akuya, me za ta yi ba barna ba! Ta yaya wadanda suka zauna suka shata lalata al’amurra a ce su ne kuma za su sake zama domin gyara lamurra, alhali tunda farko sun lalata ne domin su amfana? Ta yaya wadanda ke faman shan lagwada daga matsalolin da kasar ke ciki za su so a samar wa kasar makomar da ta dace, su kuma a yi waje da su, tasu makomar ta shiga tasku!
Saboda haka ni ina ganin tun da farko da Shugaban kasa Jonathan da shugaban Majalisar Datttijai Dabid Mark da ma duk masu ikirarin a tattauna makomar kasar ba don Allah suke wannan kira ba, suna kuma sane cewa taron ba zai haifar da da mai ido ba, amma da yake sun saba wasan kura da sauran mutanen kasar, za su shirya taron bogi, su kashe dukiyar kasa, a kuma koma gidan jiya. Hakan kuwa zai kasance ne saboda kawai giyar mulki da son dawwama bisa mulki ta kowane irin hali. Shi ya sa wasu ke cewa dukkan niyyar taron ba ta wuce zaben 2015, da zarar aka cimma manufa, komai zai koma kamar da dai ba a tattauna ba.
Saboda haka, idan dai taron makomar kasa ake son a yi na gaskiya, to ba wadannan ’yan siyasar da masu mulki da ilimin da muke da su ne za su gudanar da shi ba. Haka kuma ba attajirai da ’yan kwangilar da muke da su za su hallara a wurin taron ba, domin kuwa daga cikin wadannan gungun ’yan Najeriyar ne ake samun masu gurgunta kasar har ta rasa makoma. Ba wadanda suka dace da halartar taron makomar kasar sai wadannan mutane da ke cikin kasar nan.
•Mutane sama da miliyan 60 da ke da tabuwar hankali a cikin kasar nan saboda tsarin miyagun shugabanni.
•Mutane sama da miliyan 80 da ke kwana da tashi cikin talauci da rashi da fatara da yunwa.
•Mutane sama da miliyan 21da ke yawo da watangaririya ba aikin yi ko sana’ar da za su samu na toshe uwar hanji
•Mutane sama da miliyan 50 da ke shiga da fita cikin harkar karatu tun daga firamare har zuwa jami’a, amma maimakon ilimi ya shige su, sai dai su yi hannun riga da shi.
•Mutane sama da miliyan 40 da ba su da wurin kwana, ko magudanun ruwan kwarai ko titunan kwarai ko sauran abubuwan more rayuwa.
•Mutane sama da miliyan 30 da sun kasa yin aure, wadanda suka yi daga cikinsu, sun kasa zaman auren, wadansu daga cikinsu, ba su san wani abu ba face, fyade da madigo da ludu.
Idan wadannan miliyoyin jama’a sun taru a Abuja ina jin su ne za su iya tattauna makomar kasar, domin su ne suka san inda dakin ke yoyo, ba barayin zaune ko cima-zaunen ’yan siyasa da masu mulki da attajiran da ba su san Annabi ya faku ba.
Za mu ci gaba