✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taron wayar da kan ’yan jarida ya rikide zuwa na siyasa a Jigawa

Taron wayar da kai kan hanyoyin sadarwa da yada labarai na zamani da Kungiyar ’Yan jarida ta Kasa (NUJ) reshen Jihar Jigawa ta shirya wa…

Taron wayar da kai kan hanyoyin sadarwa da yada labarai na zamani da Kungiyar ’Yan jarida ta Kasa (NUJ) reshen Jihar Jigawa ta shirya wa manema labarai da masu amfani da facebook da sauran hanyoyin sadarwa na zamani a cibiyar ’yan jarida ta Jihar Jigawa ya yi kusan komawa taron siyasa.

Hakan ya faru ne a lokacin da dan Majalisar mai wakiltar Karamar Hukumar Dutse a Majalissar Dokokin Jihar Jigawa Alhaji Musa Sule Dutse ya amshi abin magana, inda ya fara da kalubalantar ’yan jarida kan buga labarai marasa sahihanci, ya danganta su da marasa kan gado da rashin amfani da dokar yada labarai.

Ya kara da cewa dokar soja ta 47 ita ce dokar da ta yi wa ’yan jarida daidai, inda duk wanda ya yi kalamai na batanci a kan shugaba za a daure shi, amma yanzu saboda an raina gwamnati ’yan jarida ba su san mutuncin shugabanninsu, sai su rubuta abin da suka ga dama ba a daure su ba, ko a hukunta su, shi ya sa suke zagin kowa a Najeriya saboda rashin doka.

Alhaji Musa Sule ya kara da cewa kamata ya yi duk dan jaridar da ya yi rubutu a kan wani dan siyasa ya bata mai suna ko ya zargi Shugaban Kasa a daure shi ba beli. Kuma ya nemi a sa wa sauran kafafan watsa labarai takunkumi saboda masu rubutu da suke amfani da wadancan hanyoyin sadarwa na zamani.

Gama kalamansa ke da wuya sai tsohon mai magana da yawun tsohon Gwamnan Jihar Jigawa na Jam’iyyar PDP Malam Umar Kiyari Jitau Madamuwa wanda shi ma tsohon dan jarida ne ya amshi abin magana, inda ya ce abin da dan majalisar ya fada bai yi wa ’yan jarida adalci ba, kuma hakan ya saba wa dokar soja na aikin jarida a lokacin Janar Babangida da zamanin Buhari yana soja.

Ya kara da cewa a wancan lokacin an yi amfani da dokar soja an ci zarafin ’yan jarida an danne musu hakki, an hana su magana, domin dan jarida ba ya da ikon fadar gaskiya, yanzu kuwa siyasa ake babu wanda ya isa ya hana manema labarai aikinsu muddin za su tsaya kan gaskiya. Kwamared Kiyari ya kara da cewa, ’yan jarida ka da ku ji tsoro a kan aikinku na tsage gaskiya komai daci, ku fito ku fadi gaskiya ku yi aikinku.

Shi kuma tsohon Manajan Gidan Rediyon Freedom kuma tsohon ma’aikacin BBC, Danmasanin Dutse kuma Hakimin Dutse Alhaji Adamu Aliyu Kiyawa cewa ya yi abin da aikin jarida ke so ya zama wanda ke aikin mutum ne mai yawan karance-karance saboda aiki ne da ke bukatar haka, sannan ya ce aikin yana bukatar sha’awa ba wai karatu kadai ba.